Bayan Mijinta Ya Gaza a Gado, Wata Matar Aure Ta Jaraba Kwazon Direba, Ta Samu Ciki

Bayan Mijinta Ya Gaza a Gado, Wata Matar Aure Ta Jaraba Kwazon Direba, Ta Samu Ciki

  • Wata matar aure ta fito ta bayyana yadda ta ci amanar Mijinta lokuta da dama a yunkurinta na ganin ta zama uwa
  • A cewar wani Bidiyon da matar ta amsa laifinta, Matar ta ƙulla alaƙa mai ƙarfi da Direbanta kuma har ta haifi yara guda biyu
  • A halin yanzun dai ta shiga yanayin ruɗani saboda tsoron wataran Mijin ya gano cewa ba shi ne mahaifin 'ya'yanta biyu ba

Wata matar aure a ƙasar Ghana da bayyana yadda ta kulla alaƙa tare da gwada kwazon direbanta, wanda a yanzu shi ne mahaifin 'ya'ya biyu da Allah ya bata.

Yayin da lamarin ya hanata sukuni, matar ta yi amfani da kafar Talajin TV3 Ghana wajen labarta yadda direba ya ɗirka mata ciki har sau biyu.

Matsalolin aure.
Bayan Mijinta Ya Gaza a Gado, Wata Matar Aure Ta Jaraba Kwazon Direba, Ta Samu Ciki Hoto: Gettyimages
Asali: Getty Images

Da take faɗin yadda lamarin ya faru, Matar wacce aka ɓoye bayananta saboda halin rayuwa, tace ta Auri sahibinta tsawon shekaru Shida amma shiru bata ɗauki juna biyu ba.

Kara karanta wannan

Yadda Naga Matata Tana Saduwa da Ɗan Uwana, Miji Ya Faɗa Wa Kotu Komai, Ya Nemi Raba Auren

Sakamakon haka ta garzaya wurin likita domin ya duba abinda ke damunta amma ya shaida mata cewa babu wata matsalar da zata hanata ɗaukar ciki a tare da ita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai a ɓangarensa, Mijinta ya ƙi yarda ya je Likita ya duba lafiyarsa domin lalubo inda matsalar take.

Ta kulla alaƙa da Direbanta

Da take ci gaba da bayyana labarinta, Matar tace daga nan ta kulla alaƙar abokantaka mai ƙarfi da Direbanta wanda ta kira da mutum mai daɗin sha'ani.

Alaƙarsu ta cigaba da ƙara danko har ya dirka mata ciki kuma bayan ta haife ɗan sai ta sake samun ciki karo na biyu duka a wurin Direban.

Kallo Bidiyon anan

Masu amfani da Youtube sun faɗi ra'ayoyinsu

Ernest Gyamfi yace:

"Idan nine zan karɓi yaran na maida su tamkar nine mahaifinsu, dama mutane kan ɗauki marayu su maida su tamkar 'ya'yan cikinsu."

Kara karanta wannan

Matashi Dan Najeriya Ya Nunawa Duniya Kyakkyawar Budurwarsa Farar Fata Tana Rangada Masa Girki a Bidiyo

Kwetey Richard Tetteh yace:

"Wow abu ya yi kyau, mun gode Allah ta faɗi gaskiya da bakinta."

A wani labarin kuma Wata Hamshakiyar Mai Kudi a Abuja Na Neman Wanda Zai Dirka Mata Ciki, Zata Biya N3m

Wata Mai kuɗi dake zaune a Birnin tarayya Abuja ta shiga neman kyakkyawan Saurayin da zai iya ɗirka mata ciki.

Attajirar ta yi alkawari baiwa duk wanda iya wannan aiki kuɗi naira Miliyan Uku amma akwai sharuddan da ta kafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel