Rishi Sunak: Abubuwa Masu Daukar Hankali 7 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Firayiministan Burtaniya

Rishi Sunak: Abubuwa Masu Daukar Hankali 7 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Firayiministan Burtaniya

A yau 24 ga watan Oktoba ne labarai suka mamaye kafafen yada labarai na duniya kan cewa, kasar Burtaniya ta yi sabon Firayinminista, bayan da Liz Truss ta ajiye aikinta.

Babban lamari ne ga nahiyar Turai da kuma kasar Burtaniyya a bangare guda samar da Rishi Sunak a matsayin sabon Firayinministan kasar.

Daga sunansa, akwai sirkin Indiyanci a ciki, to amma me kuka sani game dashi? Mun tattaaro muku kadan daga rayuwarsa mai daukar hankali.

Tarihin Rishi Sunak, wanda ya zama sabon firayinministan Burtaniya
Rishi Sunak: Abubuwa Masu Daukar Hankali 7 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Firayiministan Burtaniya | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

1. Haihuwarsa

An haifi Sunak a ranar 12 ga watan Mayun 1980 a Southampton ta birnin Ingila, kuma iyayensa Indiyawa ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sunak mabiyin addinin Hindu ne, kuma da littafin Bhagavad Gita ya yi rantsuwa lokacin da ya zama mamban majalisa (MP), inji rahoton Business Standard.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Rishi Sunak Ya Zama Sabon Firayim Ministan Birtaniya

2. Nasabarsa

Iyayensa sun kasance 'yan gudun hijiran da suka shigo Burtaniya daga Gabashin Afrika a shekarar 1960.

Iyayen nasa dai sune Yashvir da Usha Sunak, kamar yadda The Quint ta tattaro tarihinsu.

3. Karatunsa

Ya karanta ilimin falsafa, siyasa da tattalin arziki a kwalejin Lincoln dake Oxford a 2001.

Ya yi digiri na biyu a fannin gudanar da kasuwanci a jami'ar Standford dake birnin Amurka a 2006.

4. Aurensa

A watan Agustan 2009, Sunak ya auri Akshata Murthy, diyar hamshakin attajirin nan dan kasar Indiya N.R Narayana Murthy.

Sirikin Sunak ne mai katafaren kamfanin nan na Infosys; sananne a duniya, rahoton The Telegraph.

5. Shirin rike ma'aikata

Sunak ya kirkiro wani shirin da ya tanadi £330bn na ko-ta-kwana ga kasuwanni don tallafawa ma'aikata.

Ya kirkiri wannan shirin ne a ranar 17 ga watan Maris na 2023 don ba ma'aikata kwarin gwiwar ci gaba da zama a ma'aikatun da suke aiki, duba rahoton BBC News.

Kara karanta wannan

Yanzu Haka: Buhari Ya Karrama Jonathan, Wike Da Wasu Mutum 42 Da Lambar Yabo

6. Alakarsa da kudi da mulki a Burtaniya

Bugu da kari, Rishi Sunak ya kasance ministan kudin Burtaniya daga ranar 13 ga watan Fabrairun 2020 zuwa 5 ga wtaan Yulin 2022 a karkashin gwamnatin Boris Johnson.

Ya kuma rike mukamai da dama a kasar tun a daga shekarar 2014.

7. Ya zama Firayinminista

A yau, 24 ga watan Oktoba, ya lashe kujerar zama sabon Firayinministan kasar Burtaniya, kamar yadda majiyoyi da dama suka yada.

Ya samu wannan dama ne kasa da mako guda kenan da tsohuwar Firayinministan Burtaniya, Liz Truss ta yi murabus.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.