Sojan Da Ya Yi Gadin Gawar Sarauniya Elizabeth Ta II Ya Rasu

Sojan Da Ya Yi Gadin Gawar Sarauniya Elizabeth Ta II Ya Rasu

  • Kwanaki kadan bayan rasuwar Sarauniya Elizabeth ta II, wani abin bakin ciki ya sake faruwa a Birtaniya
  • An tsinci gawar, Trooper Jack Burnell-Williams, dan shekara 18 wanda ya yi gadin gawar sarauniya
  • Rahotanni sun bayyana cewa an gano gawar matashin ne a Barikin Hyde Park a Knightsbridge, a Landan

Birtaniya, Landan - Trooper Jack Burnell-Williams, matashi dan shekara 18 wanda ya yi gadin gawar Sarauniya Elizabeth ta II a wurin jana'izarta ya rasu.

A cewar The Telegraph, an gano gawar matashin ne a Barikin Hyde Park a Knightsbridge, Landan a ranar Laraba 28 ga watan Satumba.

Sojan da ya yi gadin gawar Sarauniya.
Sojan Da Ya Yi Gadin Gawar Sarauniya Elizabeth Ta II Ya Rasu. Hoto: Photo: The Telegraph and Wikimedia Commons.
Asali: UGC

Legit.ng ta tattaro cewa an kira wasu ma'aikatan lafiya wurin da abin ya faru kafin suka tabbatar ya rasu.

Mahaifiyar matashin dan shekara 18 da sojoji sun yi alhinsa

Kara karanta wannan

Babachir Lawal Bai Taba Tsayawa Kiristoci ba Yayin da yake SGF, Limamin Kirista Yayi Tone-tone

Mahaifiyarsa, daga Bridgend, South Wales, ta yi alhinin rashinsa ta hanyar wallafa hotonsa a soshiyal midiya sanye da unifom dinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta rubuta:

"Ban taba tunanin zan fada haka ba amma mu a matsayin iyali muna alhinin rashin dan mu."

Kafin rasuwarsa, iyalansa sun wallafa bidiyon dogarin a wurin bikin jana'izar sarauniya, tana cewa 'muna alfahari' da Mr Burnell-Williams saboda 'yi wa sarauniya rakiya zuwa gidanta na gaskiya.'

Za a saki balan-balan don karrama shi a wannan makon

Kakakin Metropolitan Police ya ce:

"An kira yan sanda misalin karfe 3:48 a ranar Laraba 28 ga watan Satumba cewa an tsinci wani mutum baya numfashi a Barikin Hyde Park.
"Jami'an mu tare da motar kai daukin gaggawa suka tafi. An tabbatar da wani mutum dan shekara 18 ya rasu. An sanar da yan uwansa."

Kakakin yan sanda ya ce:

Kara karanta wannan

Rudani yayin da'yan bindiga suka mudun shinkafa, wake da jarkar manja a matsayin fansa a Kaduna

"Muna bakin cikin tabbatar da rasuwar Trooper Jack Burnell-Williams a ranar 28 ga watan Satumba a Hyde Park Barracks. Muna mika ta'aziyya ga iyalan sojan da abokansa a wannan lokacin."

"Ba A Barin Matan Najeriya A Baya": Hotunan Matan Najeriya Sanye Da Anko Na Jana'izar Sarauniya Ya Kayatar

A wani rahoton, wasu mata yan Najeriya a baya-bayan nan sun wakilci kasar a wurin jana'izar sarauniya Elizabeth II.

Kwararren dan jarida, Dele Momodu, ya wallafa wasu hotuna a dandalin sada zumuna inda ya nuna matan Najeriya sanye da anko a wurin jana'izar Sarauniya Elizabth ta II.

Asali: Legit.ng

Online view pixel