An Bayyana Abinda Ya Haddasa Mutuwar Sarauniyar Ingila Queen Elizabeth II
- A ranar 29 ga watan Satumba, 2022 aka bayyana takaradar shaidar mutuwar Sarauniya mafi daɗe wa a tarihin masarautar Ingila
- Takardar ta bayyana cewa Sarauniya ta rasa rayuwarta ne sandiyyar tsufa, ta mutu tana da shekara 96 a duniya
- Sarauniyar wacce ta shafe shekara 70 a karagar mulki ta mutu ne ranar 8 ga watan Satumaba, 2022 a fadar Balmoral
Musabbabin abinda ya haddasa mutuwar Basarakiyar Birtaniya, Sarauniya Elizabeth ta II ya bayyana. A bayanan da ke ƙunshe a takardar shaidar mutuwarta, ya nuna cewa tsufa ne ya yi ajalin Sarauniya.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Sarauniya Elizabeth ta II ta mutu ne tana da shekaru 96 a duniya a fadar Balmoral yayin da iyalan gidan Sarautar ke kewaye da ita a farkon watan nan.
A takardar shaidar da National Records of Scotland ta fitar ranar Alhamis, 29 ga watan Satumba, 2022, marigayya Sarauniya ta mutu ne da ƙarfe 3:10 na yamma ranar 8 ga watan Satumba, 2022 a Fadar Balmoral, Ballater.
Musabbabin abinda ya haddasa mutuwar Sarauniya shi ne tsufa kamar yadda ka rubuta ɓaro-ɓaro a takardar kuma masarautar Ingila ta rattaɓa hannu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Labarin mutuwar Saraunuya ya fito ne a wata sanarwa da Masarautar Ingila ta fitar a madadin iyalan Elizabeth ta II.
"Sarauniya ta mutu cikin kwanciyar hankali a fadar Balmoral da yammacin nan. Sarki da Sarauniya za su zauna a Balmoral da yammaci kuma gobe za su koma Landan," inji Sanarwan.
Elizabeth II ta kwashe shekara 70 a gadon sarauta
Mutuwarta ya kawo karshen shekaru 70 da ta yi a karagar mulki, Basarakiya mafi daɗe wa a tarihin masarautar Ingila. Ta karɓi mulki ne bayan mutuwar mahaifinta Sarki George na IV a ranar 6 ga watan Fabrairu 1952.
An haifi marigayya Elizabeth a ranar 21 ga watan Afrilu, 1926 lokacin mulkin Kakanta, Sarki George na V. Queen Elizabeth II ta zama Sarauniya mafi daɗe wa a karagar mulki.
An yi shagalin murnar cikar Sarauniya Elizabeth ta II shekara 70 a kan sarauta ranar 6 ga watan Fabrairu.
A wani labarin kuma Allah Ya Yiwa Sarkin Lokoja, Jihar Kogi, Dr Muhammadu Maikarfi, rasuwa
Dr. Muhammadu Kabir Maikarfi III ya rasu ne ranar Laraba a birnin tarayya Abuja bayan gajeruwar rashin lafiya da yayi.
Majiyoyi sun bayyana cewa za'a yi jana'izar mamacin ne ranar Alhamis, 29 ga watan Satumba, 2022 a Lokoja, babbar birnin jihar Kogi misalin karfe 4 na yamma.
Asali: Legit.ng