Daga Na 5 Ya Koma 20: Hamshakin Attajirin Duniya Ya Rasa Kaso 50 Na Dukiyarsa a 2022
- Mai kamfanin Facebook, Mark Zuckerberg, ya yi asarar damin kuɗi fiye da sauran hamshakan attajiran duniya
- Fitaccen mai fasahar ta zamani ya gamu da karayar Arziki inda dukiyarsa ta ragu daga dala Biliyan $152bn a 2021 zuwa $56bn a 2022
- Attajirin duniyar ya rasa kusan Dala Biliyam $71 a dukiyarsa, wanda ya kai kaso 50% yayin da kamfaninsa ya maida hankali kan Metaverse
Hamshakin Attijirin nan mai kamfanin sada zumunta Facebook, wanda yanzun ya koma Meta, Mark Zuckerberg, ya gamu da karayar arziki yayin da dukiyarsa ta sauka da dala biliyan $71bn tun bayan shiga shekarar 2022.
Manyan masu kuɗi a fannin fasaha sun samu karayar arziƙi, amma karayar Arzikin Zuckerberg ta fi muni daga cikinsu.
Daga na 5 ya koma na 20 a Attajiran duniya
Dukiyarsa ta yi ƙasa da sama da kashi 50 daga lokacin da ta yi zarra zuwa dala biliyan $152bn a watan Satumba, 2022. Har yanzun Zuckerberg na da Arzikin $56bn amma ba ya cikin Hamshakan Attajiran duniya na sahun farko.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A halin yanzun, mamallakin Kamfanin Facebook ya koma na 20 a jerin masu kuɗin duniya, matsayi mafi ƙasa da aka taɓa ganinsa a jerin Biliyoniyoyin da Bloomberg ta saba fitarwa tun 2014.
Mafi yawan dukiyar masu kasuwancin Metaverse ta baibaye kamfanin Meta yayin da kusan hannun jari miliyan 350, canza tsarin kasuwanci da sauran wasu dalilai suka haddasa faɗuwar farashin hannun jarin Kamfanin warwas.
Metaverse ke durƙusad da arzikin Meta
Mark Zukerberg ya amince cewa masu hannun jari dake ƙara zuba dukiyarsu a tsarin Metaverse sun kara jawo wa Kamfanin asarar kuɗaɗe masu yawa cikin ƙanƙanin lokaci.
A cewar wani daga kamfanin, Ma'aikata sun bayyana cewa a halin yanzun Attajirin ya maida hankali kan Metaverse kaɗai.
Chief Operating Officer na kamfanin Facebook da ya shafe tsawon lokaci, Sheryl Sandberg, da kuma Injiniyan dake kula da tsarin baya na tallace-tallace duk sun bar kamfanin a wannan shekarar.
Hotunan Fasto Yana Raba Wa Almajirai Allo Da Kayan Karatu A Kaduna Don Bikin Ranar Zaman Lafiya Ta Duniya
Canza tsari bai da amfani
Kirkiran sabon tsarin faifan Bidiyo a Facebook da Instagram 'Reesls' bai iya daƙile bunƙasar Manhajar TikTok ba, haka nan Facebook ya rasa mutane da dama a kwata ta biyu a 2022.
Darajar arzikin Kamfanin ta kai kusan $147 a duk hannun jari ɗaya, ta yi ƙasa sosai daga $340 da take a farkon shekarar 2022.
Kamar dai yadda ta faru da Meta, sauran manyan kamfanonin fasaha kamar Amazon da Google na fama da matsalolo a shekarar nan amma ba su shiga tsaka mai wuya ba.
A rahoton da Bloomberg ta fitar, Mark Zuckerberg ya gwada wasu dabarun kamar bayya aa shirin Joe Rogan za kuwa su bidiyo da aka ganshi yana gwana zane-zane.
A wani labarin kuma mu tattara muku Jerin Kananan Yara 10 Mafi Arziki a Duniya, Shekarunsu, Dukiyar da Suka Mallaka da Iyayensu
Wasu shahararrun yara masu arziki suna tara dukiyarsu ne da guminsu yayin da wasu kan samu nasu ne ta hanyar gada daga iyayensu.
Mafi kankanta a cikin yaran shekarunsa 4 a duniya, kuma babban cikinsu shekarunsa 17, sun tara kudinsu ne ta hanyar aiki tukuru.
Asali: Legit.ng