Elizabeth II: Shugaba A Afirka Ya Ayyana Zaman Makoki Na Kwana 3 Don Jimamin Rasuwar Sarauniyar Birtaniya

Elizabeth II: Shugaba A Afirka Ya Ayyana Zaman Makoki Na Kwana 3 Don Jimamin Rasuwar Sarauniyar Birtaniya

  • Uhuru Kenyatta, shugaban kasar Kenya mai barin gado ya ayyana zaman makoki na kwana uku a kasarsa saboda rasuwar Sarauniya Elizabeth ta II
  • Kenyatta ya bada umurnin a sauke tutoci zuwa rabi a gidan gwamnati, sansanin sojoji, gine-ginen gwamnati na cikin gida da kasashen waje tsawon kwanakin
  • Shugaban na Kenya ya kuma mika sakon ta'aziyya ga iyalan Sarauniya Elizabeth II da daukakin al'ummar kasar Birtaniya kan rashin sarauniyar wacce ta fi kowa dadewa kan gadon sarautar kasar

Kenya - Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya ayyana kwanaki uku na hutu don a kasarsa don zaman makoki na rasuwar Sarauniya Elizabeth II, NTV ta rahoto.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a, shugaban kasar mai barin gado ya ce zaman makokin zai fara ne daga ranar Juma'a 9 ga watan Satumba zuwa Litinin 12 ga watan Satumban 2022.

Kara karanta wannan

Zaben Ekiti da Osun: INEC ta ce wasu madatsa sun farmaki tashar yanar gizonta

Kenyatta da Elizabeth II
Elizabeth II: Shugaba A Afirka Ya Ayyana Zaman Makoki Na Kwana 3 Don Jimamin Rasuwar Sarauniyar Birtaniya. Hoto: NTV.
Asali: Facebook

Shugaba Kenyatta ya umurci dukkan hukumomin gwamnati kasar da na gida da kasashen waje su tabbatar sun saukar da tutoci da ke harabarsu zuwa rabi na tsawon kwanakin uku.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugaba Kenyatta ya ce:

"Za a saukar da tutun Jamuriyar Kenya zuwa rabi a gidan gwamnati da sauran ofisoshin diflomasiyya, gine-ginen gwamnati, sansanin sojoji da tashohi da jiragen sojojin ruwa, da ma ko ina a Jamhuriyar Kenya, daga asubahin yau zuwa faduwar rana ta Litinin 12 ga watan Satumban 2022."

Kenyatta mika sakon ta'aziyya ga iyalan Sarauniya Elizabeth da mutanen Birtaniya

Yayin da ya ke aika sakon ta'aziyya ga iyalan sarauniyar da mutanen Birtaniya, Shugaba Kenyatta ya jinjinawa sarauniyar a matsayin jajirtaciyyar shugaba wacce tarihi zai rika tunawa da ita a matsayin daya cikin yan gidan saurata da suka hidimtawa duniya.

Sarauniya Elizabeth ta II, itace ce wacce ta fi dadewa kan gadon sarauta a tarihin Birtaniya, ta kuma rasu ne a ranar 8 ga watan Satumban 22, tana da shekaru 96 a Balmoral, Scotland.

Kara karanta wannan

Shugaban wata kasa mai karfin iko ya ce ba zai halarci bikin bison sarauniyar Ingila ba

Kenya na daya cikin kasashe 36 da Birtaniya ta raina wacce sarauniyar ke matsayin shugaba a wurinsu.

Sarauniya Elizabeth Ta II: Abubuwa 5 Da Za Su Faru Yanzu Bayan Mutuwar Sarauniyar Mafi Dadewa Kan Mulki

Kafin sanarwar rasuwarta, mutane a fadin duniya sun shiga yanayin damuwa bayan da fadar Buckingham ta sanar cewa likitoci na duba Sarauniya Elizabeth ta II a Scotland.

Wasu da dama kuma sun ce sanarwar da fadar gidan sarauntan na Birtaniya ya fitar, wacce ya ce likitoci sun damu da halin da ta ke ciki ya nuna rashin lafiyar ya yi tsanani.

Amma, Fadar ta Buckingham ta sanar cewa Sarauniyar ta rasu cikin salama a barcinta a ranar Alhamis a Balmoral, a gidan sarauta a Scotland.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164