Hotunan Atamfofin da 'Yan Najeriya Suka Fitar Matsayin Ankon Bikin Mutuwar Sarauniyar Ingila
- 'Yan Najeriya a soshiyal midiya sun bayyana martani daban-daban kan mutuwar Sarauniya Elizabeth II ta Ingila
- Idan za a tuna, basarakiyar ta kwashe sama da shekaru 70 tana kan karagar mulkin kafin ta rasu a ranar Alhamis
- Jim kadan bayan rasuwarta, 'yan Najeriya sun bayyana hotunan atamfofi masu dauke da hoton sarauniyar matsayin ankon bikin mutuwarta.
In har a wurin nishadi ne, ba a wuce 'yan Najeriya kuma ko da ake cikin tsananin makoki da kunar mutuwar Sarauniyar Ingila Elizabeth, sun cigaba da ba mutane dariya da salonsu.
Sarauniya Elizabeth II ta rasu a ranar Alhamis, 8 ga watan Satumban 2022 yayin da take da shekaru 96 a duniya.
Kamar yadda dai aka saba a Najeriya, ana yin ankon atamfa ko leshi a yayin bukukuwan mutuwa wanda 'yan uwa da abokan arzikin mamatan ke sanyawa.
Toh a wannan ma ba a bar 'yan Najeriya a baya ba, sun yanke hukuncin fitar da nako mai hoton sarauniyar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Shafin @goldmyne ne suka wallafa a Instagram cike da barkwanci yayin da ake bayyana kudin ankon ga masu son siya.
Duba wallafar:
'Yan Najeriya sun yi martani kan ankon mutuwar Sarauniya
pisax_marcel:
"Don Allah ya za a yi in siya har da Aso Oke da cikakken kallabin? Tamkar mahaifiya take a wurina."
realhonestmax:
"Komai zan iya yi saboda sarauniyarmu, nawa ne atamfar?
goalgetter3571:
"Bai fa cika ba saboda ba a hada da kudin visa da na jirgi ba."
unknown_hf.xx:
"Mutane sun fara haukacewa a kan wannan lamarin."
Kyawawan Hotunan Lokuta da Rayuwar Marigayiyar Sarauniya Elizabeth II
A labari na daban, Ingila ta fada makoki a ranar Alhamis, 8 ga watan Satumban 2022 bayan labarin mutuwar sarauniya Elizabeth Alexandra Mary wacce ta kasance sarauniyar da ta fi kowanne sarki dadewa a kujerar sarautar Birtaniya.
Mahaifiya kuma kakar an haifeta a ranar 21 ga watan Afirilin 1926 a titin Bruton dake Landan, UK ga tsohon Duke din York, Yarima Albert da matarsa Elizabeth Bowes-Lyon.
Kamar yadda takardar da fadar Buckingham ta fitar ta bayyana,sarauniyar ta tabbata basarakiyar da tafi dadewa a kujerar tun a 2015 yayin da ta wuce shekarun da Sarauniya Victoria tayi a kujerar.
Asali: Legit.ng