Jerin Kasashen Afirka 10 Da Suka Samu Yancinsu A Zamanin Mulkin Sarauniya Elizabeth II

Jerin Kasashen Afirka 10 Da Suka Samu Yancinsu A Zamanin Mulkin Sarauniya Elizabeth II

  • Mulkin Sarauniyar Ingila Elizabeth ta Birtaniya na cike da abubuwa na tarihi da za a dade ba a manta da su ba
  • A shekaru 70 da ta yi a matsayin mai mulkar Ireland, Scotland, England da Wales, ta kuma karfafa zumunci da nahiyar Afirka
  • Sarauniya Elizabeth ne ta bada yancin kai ga wasu kasashen Afirka goma ciki har da Najeriya, Afirka ta Kudu, Ghana, Kenya da wasu

A yayin da duniya ke juyayin rasuwar Sarauniya Elizabeth II, wani muhimmin lamari ba za a iya mantawa ba shine tarihin da sauraniyar ta kafa na yantar da kasashe a duniya.

A zamanin mulkin ta a matsayin shugaban Birtaniya, sarauniyar ta bawa kasashen Afrika guda goma yancin kai.

Sauraniyar Ingila Elizabeth
Jerin Kasashen Afirka Da Suka Samu Yanci Karkashin Mulkin Sarauniya Elizabeth II. Hoto: BBC
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Yadda Hannu a Karbar Kudin Fansa har N2b da Alaka da Kungiyar Ta'addanci ta sa aka Kama Mamu

A wannan rahoton, Legit.ng za ta yi waiwaye ta kawo jerin wadannan kasashen na Afirka da shekarun da suka samu yanci a matsayin kasashe masu cin gashin kansu.

1. Gambia

Gambia na daya cikin manyan kasahen Afirka ta yamma.

A cewar alkalluma daga Bankin Duniya a 2020, adadin mutanen da ke kasar sun kai miliyan 2.417.

Kasar ta Gambia na cikin kasashen da ke karkashin mulkin Birtaniya kafin ta samu yanci a shekarar 1965. Babban birnin kasar ita ce Banjul kuma shugaban ta na farko shine Sir Dawda Kairaba Jawara.

2. Ghana

Ghana, wacce a baya ake kira Gold Coast kasa ce a nahiyar Afirka ta Yamma kuma tana cikin kasashen da Birtaniya ta raina.

Kasar na da ma'adanun kasa da dama musamman gwal.

Yawan mutanen kasar sun haura miliyan 31.07 kuma tana da iyaka da kasashen Ivory Coast, Burkina Faso da Jamhuriyar Togo.

A ranar 6 ga watan Maris na 1957, Ghana ta samu yanci kuma a ranar 1 ga watan Yulin 1960, ta zama Jamhuriya da shugabanta na farko Kwame Nkurumah.

Kara karanta wannan

Babban lauya ya fusata, yana son ganin Buhari a gaban kotu saboda harin Kuje

3. Kenya

Kenya kasa ce ta ke Afirka ta Gabas da adadin mutane fiye da miliyan 54.

Kasa ce da mutanen ta ke da al'adu da tarihi na daruruwan shekaru.

Kenya ta samu yancinta daga Birtaniya a ranar 12 ga watan Disambar 1964 kuma Jomo Kenyatta ya zama shugabanta na farko.

4. Malawi

Ita ma a Afirka ta Gabas ta ke kamar Kenya, Jamhuriyar Malawi karamar kasa ce mai yawan mutane fiye da miliyan 20.

Tana da iyaka da Zambia ya yamma, Tanzania ta arewa da arewa maso gabas, da Mozambique ta gabas, kudu, da kudu maso yamma.

Malawi ta samu yanci daga Birtaniya a ranar 6 g watan Yulin 1964, kuma Hastings Banda ne shugabanta na farko.

5. Mauritius

Mauritius tsibiri na Tekun Indiya, mutanen kasar da kadan suka dara miliyan 2.

Babban birnin kasar ita ce Port Louis kuma ta samu yancinta daga Birtaniya a ranar 12 ga watan Maris na 1968.

Kara karanta wannan

Yanzu Nan: DSS ta Magantu Kan Cafke Mamu, Ta Bayyana Dalilinta

Sir Seewoosagur Ramgoolam ne ya zama farai ministanta na farko.

6. Najeriya

Najeriya, kasa ce da ake yi wa lakabi da giwan Afirka saboda wurin da ta ke a taswirar Afirka.

Jamhuriyar Tarayyar Najeriya mai yawan al'umma fiye da miliyan 250 ta samu yancinta daga Birtaniya a ranar 1 ga watan Oktoban 1960 kuma ta zama Jamhuriya a ranar 1 ga watan Oktoban 1963.

Najeriya ce kasa mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka, kuma babban birnin kasar ita ce Abuja.

7. Rhodesia (Zimbabwe)

Zimbabwe, wacce a baya ake kira Rhodesia tana kudancin Afirka ne. Tana da mutane fiye a miliyan 15.

Ita ma tana cikin kasashen da ke karkashin mulkin Birtaniya.

Babban birnin kasar ita ce Harare kuma a ranar 11 ga watan Nuwamban 1965, an rattaba hannu kan bata yanci, Zimbabwe ta zama Jamhuriya a 1970, Canaan Banana ya zama shugabanta na farko yayin da Robert Mugabe ya zama farai ministan farko.

Kara karanta wannan

Hotunan Ummi, Kyakkyawar Budurwar Da Ta Rasa Ranta A Farmakin Da Yan Bindiga Suka Kai Bankunan Kogi

8. Sierra Leone

Sierra Leone karamar kasa ce a Afirka ta Yamma da mutane kasa da miliyan 10, babban birnin kasar ita ce Freetown, kuma a baya karkashin mulkin Birtaniya ta ke.

A ranar 27 ga watan Afrilu, Sierra Leone ta zama kasa mai yanci kuma Sir Milton Margai ya zama shugabanta na farko.

9. Afirka ta Kudu

Afirka ta Kudu ita ma wata kasa ce karkashin mulkin Birtaniya da yawan mutane fiye da miliyan 60.

Kamar Najeriya, Kenya da Ghana, ita ma Afrika ta Kudu tana da al'adu da tarihi.

Manyan biranen kasar sune Cape Town, Pretoria da Bloemfontein kuma kowanne da aikinsa.

Kasar ta samu yanci a shekarun 90s amma zabenta na farko a shekarar 1994 aka yi kuma Nelson Mandela ya zama shugabanta na farko.

10. Uganda

Uganda kasa ce a Afirka ta Gabas, babban birnin ta itace Kampala.

Uganda ta samu yancinta daga Birtaniya a ranar 9 ga watan Oktoban 1962 kuma sarauniya Elizabeth II itace shugaban kasa kuma sarauniyar Uganda.

A Oktoban 1963, Uganda ta zama Jamhuriya amma ta cigaba da zama mamba na kasashen rainon Birtaniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164