Mashahurin Mai Kudin Duniya, Elon Musk, Yace Mahaifiyarsa a Gareji Take Kwana Idan ta Kai Masa Ziyara

Mashahurin Mai Kudin Duniya, Elon Musk, Yace Mahaifiyarsa a Gareji Take Kwana Idan ta Kai Masa Ziyara

  • Babban mashahurin biloniyan duniya, Elon Musk, ya bayyana cewa mahaifiyarsa a gareji take kwana idan ta ziyarcesa a Texas
  • A baya biloniyan ya bayyana cewa ba shi da gidan kansa, tare da aboki yake kwana saboda baya son tara tarkace
  • Maye Musk ta sanar da cewa in har ta je wurin 'danta a Texas, a gareji take bacci saboda ba zai yuwu a yi ginin alfarma kusa da SpaceX ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Mashahurin mai arzikin duniya, Elon Musk, ya tabbatar da cewa mahaifiyarsa, Maye Musk, tana kwana a garejinsa ne duk lokacin da ta ziyarcesa a Texas, US.

Fitaccen biloniyan a cikin kwanakin nan yayi tsokaci kan wata wallafa da tace: "Mahaifiyar Elon Musk, Maye Musk tana kwana a gareji idan ta ziyarcesa a Texas."

Kamar yadda rahoton ya bayyana, Maye mai shekaru 74 tace 'danta bashi da ra'ayin taya tarkace ko kadan, The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Budurwa ‘Yar Najeriya Na Biyan N335k Na Hayar Daki Daya Duk Wata A UK, Ta Yi Bidiyon Cikin Gidan

Elon Musk and Mum
Mashahurin Mai Kudin Duniya, Elon Musk, Ya Tabbatar Mahaifiyarsa a Gareji Take Kwana Idan ta Kai Masa Ziyara. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Ta bayyana cewa duk lokacin da ta kai ziyara Texas, a gareji take kwana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ba zai yuwu ka yi katafaren gida a kusa da inda ake yin roka ba," ta kara da cewa.

A watan Afirilun 2022, biloniyan mai shekaru 51 da kan shi ya bayyana cewa ba shi da gidan kansa inda yace a wurin aboki yake zama.

Daga bisani ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, yana da gidan zama na haya a SpaceX wanda ya kai darajar $50,000 wanda yake kusa sa kamfaninsa a Texas.

Musk ya kara da bayyana cewa, zai iya bada dukkan wasu kadarori masu daraja a rayuwarsa domin ya sadaukar da rayuwarsa ga duniyoyi biyu, duniyar Mars da wacce muke ciki.

"Zan siyar da kusan dukkan wasu kadarorina na bayyane. Ba zan mallaki ko gida daya ba.
"Bana bukatar tsabar kudin, mallakar abubuwa kai ka kasa suke," biloniyan ya wallafa a Twitter a 2020.

Kara karanta wannan

Babban gaye: Yadda nau'in takalmin wani dan kwalisa ya girgiza mutane a intanet

Bayan ganin wallafar da yayi a kan mahaifiyarsa dake kwana a gareji duk lokacin da ta ziyarcesa, Elon Musk ya tabbatar da cewa wannan batun gaskiya ne amma yace an yi kokari sosai wurin gyara wurin.

Mamallakin Tesla din yayi martani da:

"Tabbas, amma na yi matukar kokari wurin gyara wurin."

Elon Musk ya fasa siyan Twitter, ya bayyana muhimmin dalilinsa

A wani labari na daban, Elon Musk, fitaccen biloniyan duniya kuma mamallakin Tesla Inc., yace ya janye daga cinikin kamfanin Twitter da yake yi kan kudi $44 biliyan inda ya kara da cewa kamfanin kafar sadarwan ta gaza bashi bayanai kan asusun bogi a kafar.

Musk ya sanar da hakan ne a ranar Juma'a kamar yadda Reuters ta ruwaito.

Wannan cigaban ya zo ne bayan da Twitter ta bai wa Musk damar duba "firehouse" dinta, wani kundin bayanai kan daruruwan miliyoyin wallafa na kowacce rana a watan da ya gabata.

Kara karanta wannan

Karfin hali: An kama wani sojan bogi da ke yiwa mata fashi da makami

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng