Gano Muhimmancin Likitoci Musulmi Ya Sa Za A Gina Masallaci Na Farko A Wani Gari A Canada

Gano Muhimmancin Likitoci Musulmi Ya Sa Za A Gina Masallaci Na Farko A Wani Gari A Canada

  • Mutanen garin Gander a Newfoundland da Labrador a kasar Canada sun fara aiki domin ginin masallaci na farko a garin
  • Percy Farwell, magajin garin Gander ya ce za a gina masallacin na farko ne domin kwadaitar da likitoci musulmi su zauna a garin saboda muhimmancinsu
  • Farwell ya ce tuni an samu filin da za a gina masallacin kuma suna aiki tare da wata kungiyar musulunci don kafa gidauniyar neman taimakon kudi

Canada - Garin Gander na kasar Canada a lardin Newfoundland da Labrador, suna aiki da al'ummar musulmi da ke zaune a yankunan don gina masallaci na farko a garin don kada likitoci musulmi su bar garin, rahoton Canada Today News.

Magajin garin Gander, Percy Farwell da Dakta Mohamed Barasi, Direkta na Kungiyar Al'ummar Musulmi na Newfoundland, a ranar Laraba sunce suna fatan masallacin zai karfafawa likitoci musulmi gwiwa su tsaya a garin.

Kara karanta wannan

Zan gyara fannin ilimi cikin wata shida idan na gaji Buhari, inji wani dan takara

Likitoci Musulmi
Gano Muhimmancin Likitoci Musulmi Ya Sa Za A Gina Masallaci Na Farko A Wani Gari A Canada. Hoto: Town of Gander.
Asali: Facebook

Farwell ya ce akwai kwararrun likitoci musulmi da ke aiki a Gander, kuma a baya, an rika shan wahalar shawo kansu su cigaba da zama a garin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Farwell, cikin wata hira da aka yi da shi ya ce:

"Likitoci wani bangare ne na iyali, bukatun iyali kuma ya wuce aikin da likita zai yi a matsayinsa na kwararre."

Barasi, wanda likitan kashi ne, ya ce kungiyarsa tana aiki tare da garin Gander tsawon fiye da shekara don ganin an samar da masallaci, CBC ta rahoto.

Mun samu filin da ya dace a gina masallacin, in ji shi.

Ya ce kungiyarsa yanzu tana matakin yin rajista ne a matsayin kungiyar taimakon al'umma don fara neman tallafin kudin da za a siya filin.

Mutanen garin Gander sun kai kimanin 11,600 kuma akwai asibitoci da cibiyoyin lafiya a garin.

Kara karanta wannan

Batanci Ga Annabi: Wanda Ya Kai Wa Rushdie Hari Ya Ce Ya Yi Mamakin Marubucin Jin Cewa Marbucin Bai Mutu Ba

Farwell ya kiyasta cewa akwai gidajen musulmi kimanin 55 amma ya ce za su iya kai 100 idan an hada da garuruwan da ke kewaye da su.

Musulmin dan kwallo daga Afrika ya fara gina Masallaci a birnin Seville a karo na farko cikin shekaru 700

A wani labarin, frederick Oumar Kanoute, tsohon tauraron dan wasan kwallon kafa, ya sanar da cewa, bayan kammala shiri tsaf, an fara gina katafaren Masallaci na farko a birnin Sevilla da ke kasar Spain a cikin shekaru fiye da 700.

Kanoute, Bafaranshe dan asalin kasar Mali, ya sanar da fara gina Masallacin ne bayan ya tattara dalar Amurka miliyan daya ($1m) a gidauniyar neman taimakon da ya kafa a shafin yanar gizo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel