Musulmin dan kwallo daga Afrika ya fara gina Masallaci a birnin Seville a karo na farko cikin shekaru 700

Musulmin dan kwallo daga Afrika ya fara gina Masallaci a birnin Seville a karo na farko cikin shekaru 700

- Tsohon tauraron dan wasan kwallon kafa, Frederick Oumar Kanoute, ya fara ginawa Musulman birnin Sevilla katafaren Masallaci

- Kanoute ya fara gina Masallacin daga kudaden da aka tattara a asusun neman tallafin kudi da ya kafa a yanar gizo shekara guda da ta gabata

- Katafaren ginin Masallacin mai hade da cibiyar al'adu da tarihi zai kasance irinsa na farko a tarihin birnin Sevilla a cikin shekaru fiye da 700

Frederick Oumar Kanoute, tsohon tauraron dan wasan kwallon kafa, ya sanar da cewa, bayan kammala shiri tsaf, an fara gina katafaren Masallaci na farko a birnin Sevilla da ke kasar Spain a cikin shekaru fiye da 700.

Kanoute, Bafaranshe dan asalin kasar Mali, ya sanar da fara gina Masallacin ne bayan ya tattara dalar Amurka miliyan daya ($1m) a gidauniyar neman taimakon da ya kafa a shafin yanar gizo.

Da ya ke sanar da hakan, Kanoute, dan wasa a kungiyar Sevilla FC, ya mika sakon godiya ga duk wadanda suka bayar da tallafi ta hanyoyi daban - daban.

"Ina godiya gareku, Allah ya bayar da lada ga duk wanda ya bayar da tallafi ko ya taimaka wajen yada neman taimakon kudin ginin wannan Masallaci," kamar yadda Kanoute ya wallafa a shafinsa na Tuwita bayan karewar wa'adin shekara guda na neman tallafin kudi.

Bayan Masallacin da za a gina, aikin zai hada da gina wata cibiyar al'adu da tarihi domin Musulman birnin Sevilla.

Aikin zai kasance irinsa na farko a tarihin birnin Sevilla a cikin fiye da shekaru 700.

Kanoute, wanda ya Musulunta tun yana da shekaru 20, ya shaidawa Aljazeera cewa ya sha wahalar neman Masallaci lokacin da ya koma kungiyar Sevilla FC.

Musulmin dan kwallo daga Afrika ya fara gina Masallaci a birnin Seville a karo na farko cikin shekaru 700
Kanoute
Asali: Twitter

"Na sha wahalar neman Masallaci bayan na dawo nan (Sevilla), har sai da na dinga tambayar mutane," a cewarsa.

DUBA WANNAN: FG ta bayyana matsayin Buhari a kan makomar 'yan N-Power da aka fara dauka

Ya kara da cewa akwai Musulmai fiye da 30,000 a Sevilla, yawancinsu bakin haure daga kasashen Afrika irinsu Algeria, Morocco, Senegal da Mali, sai kuma tsirarun 'yan kasar Spain da su ka musulunta.

Kafin a fara ginin katafaren Masallacin, Kanoute ya taba sayawa al'ummar Musulmi filin yin Sallah a lokacin da Musulmai ke fuskantar barazanar rasa filin sakamakon karewar kudin hayar shekara da su ka biya.

Bayan hakan ne Kanoute ya kafa gidauniyar neman tallafin ginawa Musulman Sevilla katafaren Masallaci na dun-dun-dun, irinsa na farko a tarihin birnin, domin gudanar da harkokin ibada.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng