Na Rantse Ba Zan Sake Dawowa Najeriya Ba, In Ji Mutumin Da Ke Samun Fiye Da 'N1m Duk Wata' a Turai

Na Rantse Ba Zan Sake Dawowa Najeriya Ba, In Ji Mutumin Da Ke Samun Fiye Da 'N1m Duk Wata' a Turai

  • Wani jarumi dan Najeriya da ya samu zuwa kasar Turai ya sha alwashin ba zai sake dawowa kasarsa ta haihuwa ba wato Najeriya
  • Hakan na zuwa ne bayan Akeem ya nuna irin kudaden da ya ke samu duk wata inda ya ce yana tara fiye da €1,700 wato fiye da Naira miliyan 1 kenan a yanzu
  • Jarumin wanda ke cike da annashuwa da farin ciki ya baza kudaden a teburinsa ya haska a bidiyo yana nuna wa mutane sabuwar rayuwar da ua tsinci kansa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Akeem Akintola, wani jarumi dan Najeriya da ke zaune a kasar turai, ya yanke shawarar cewa ba zai taba dawowa Najeriya ba bayan ya gano adadin kudin da ya ke samu yayin aiki a kasar waje.

A wani bidiyo da ya wallafa a dandalin sada zumunta, mutumin cikin farin ciki ya nuna kudaden Euro da ya baza a teburinsa.

Kara karanta wannan

Rikicin duniya: Jigon gwamnati ya dawo daga kasar waje, ya tarar an fara gini a cikin filinsa

Akeem Akintola.
Na Rantse Ba Zan Sake Dawowa Najeriya Ba, In Ji Mutumin Da Ke Samun Fiye Da 'N1m Duk Wata' a Turai. Hoto: @Instablog9ja.
Asali: Instagram

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Akintola ya ce ayyuka biyu ya ke yi kuma ya tara kudi €1,700 (Fiye da Naira miliyan 1) cikin wata daya.

Adetola, cike da farin ciki ya baza kudin a teburinsa, kuma ya ayyana cewa ba zai sake dawowa kasarsa ta haihuwa ba.

"Bayan aiki guda biyu na tara €1,700 a cikin wata daya, na rantse ba zan iya sake komawa Najeriya ba," in ji shi.

Matashi Mai Kafa Daya Wanda Ke Aiki A Wajen Gini Ya Samu Tallafin Karatu A Turai

A wani rahoton, Cocin Omega Power Ministries (OPM) ya sake ceto wani matashi mai fama da nakasa sannan ya sanya farin ciki a zuciyarsa ta hanyar bashi tallafin karatu a kasar waje.

Bidiyon wani matashi mai kafa daya yana aiki a wajen gini ya yadu a shafukan soshiyal midiya kuma hakan ya burge mutane da dama.

Kara karanta wannan

Bidiyon Nasiha Mai Ratsa Zuciya da Magidanci Yayi wa Matashi Bayan Ya Ganshi Yana Tadin Mota da Budurwa

Daya daga cikin wadanda bidiyon ya burge shine shugaban OPM Apostle Chibuzor Gift Chinyere wanda ya bayar da cigiyar mutum ya kuma gano shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164