So Makaho: Matashi Yayi Watsi da Kyakyawar Matarsa, Ya Auri Nakasassa, Ya Bada Dalilinsa a Bidiyo
- Amani, matashi mai shekaru 27 ya bai wa danginsa mamaki a lokacin da yayi watsi da matarsa mai lafiya inda ya kare a nakasassa
- Hukuncin matashin ya fusata danginsa wadanda suka kira shi da mahaukaci yayin da matarsa ke tsammanin budurwar ta asirce shi
- Amani yace lamarin ya fara ne a 2015 lokacin da ya fara zuwa gidan makwabtansu don ya taimaka da ayyukan karfi
Congo - Wani matashi 'dan Democratic Republic of Congo mai suna Amani, yayi watsi da kyakyawar matarsa inda ya koma kan wata budurwa nakasassa mai suna Faraji.
Amani da Faraji makwabtan juna ne amma ba hakan yasa soyayya ta kullu ba har yayi watsi da matarsa tare da makalewa budurwar mai shekaru 21.
A wata tattaunawa da Afrimax English, matashin mai shekaru 27 yace aurensa da matarsa ta farko abun wahala ne saboda kullum cikin rikici ake.
Cigaba da samun matsala a aurensu ne yasa ya fara tunanin kai ziyara makwabta inda yake taimakawa da ayyukan karfi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Amani yace a garin hakan ne ya lura da Faraji wacce take nakasassa kuma ya fada kogin sonta saboda kwanciyar hankalin da yake samu a wurinta.
Abinda ya fara tamkar abokantaka tsakanin Amaai da budurwar a 2015, ya girma a inda har yayi watsi da matarsa.
Yadda 'yan uwan Amani suka yi martani kan hukuncinsa
Amani yace 'yan uwansa sun sha mamaki da abinda yayi kuma suna masa kallon mahaukaci. Yace ba wai kin saka masa albarka kadai suka yi ba, sun ki goyon bayansa kan auren kamar yadda suka yi a baya.
Ya kara da cewa, matarsa ta farko ta fara tunanin Faraji ta asirce shi amma ba gaskiya bane. Yace:
"Lokacin da 'yan uwana suka gane cewa na bar matata ta farko saboda ita, ba su yi farin ciki ba. Sun sha mamaki kuma sun ce bani da hankali da har na yi wannan tunanin.
"Na sanar musu da cewa duk da nakasassa ce, ita nake kauna kuma nake son rayuwa da ita.
"Na yi kokarin ganar da su cewa ita ma mutum ce kuma ta cancanci soyayya. Wannan lokacin ne na yanke hukuncin zama da ita har abada."
Duk da ba su yi aure yadda ya dace ba, Amani yana da yara biyu da Faraji kuma suna rayuwa tare.
Faraji tana bukatar tallafin keken dinki saboda tana son taimakawa kanta tare da taimakon mijinta da iyalansa.
Kalla bidiyon a kasa:
Lokaci Yayi: Bayan Shekaru 11 ana Zuba Soyayya har da Haihuwar Yara 2, Masoyan Sun Angwance
A wani labari na daban, bayan kwashe shekaru 11 suna zuba soyayya kuma har suka haifa zaratan yara maza biyu masu shekaru tara da uku, masoyan juna Chaka Zulu da Emmah Chandra sun angwance.
Kamar yadda Nikani suka bayyana, su biyun sun fara soyayya a 2011 kuma sun kwashe shekaru cike da soyayyar juna tare da zama tare amma ba su yi aure ba.
Asali: Legit.ng