Lokaci Yayi: Bayan Shekaru 11 ana Zuba Soyayya har da Haihuwar Yara 2, Masoyan Sun Angwance

Lokaci Yayi: Bayan Shekaru 11 ana Zuba Soyayya har da Haihuwar Yara 2, Masoyan Sun Angwance

  • Labarin Chaka Zulu da Emmah Chanda ne ake kira da mahakurci, mawadaci idan aka yi batun soyayya da kuma auren masoya
  • Wannan za a iya alakanta shi da yadda suka kwashe shekaru 11 suna soyayya har da haihuwar yara biyu reras amma suka yi aure daga bisani
  • Soshiyal midiya sun yi martani tare da caccakar abinda yasa suka kwashe wadannan tsawon shekarun ba tare da aure ba

Bayan kwashe shekaru 11 suna zuba soyayya kuma har suka haifa zaratan yara maza biyu masu shekaru tara da uku, masoyan juna Chaka Zulu da Emmah Chandra sun angwance.

Kamar yadda Nikani suka bayyana, su biyun sun fara soyayya a 2011 kuma sun kwashe shekaru cike da soyayyar juna tare da zama tare amma ba su yi aure ba.

Kara karanta wannan

Soyayya gamon jini: Tsoho mai shekaru 93 yayi wuff da budurwarsa mai shekaru 88

Masoyan juna
Lokaci yayi: Bayan kwashe shekaru 11 ana zuba soyayya har da haihuwar yara 2, masoyan sun angwance. Hoto daga Nikani
Asali: Facebook

Chaka 'dan siyasa ne da ya kulla soyayya da 'yar jarida Emmah na tsawon shekaru 11 amma su biyun sun cigaba da rayuwa tare.

Masoyan junan an haifesu a watan Nuwamba

Bayanai sun bayyana cewa, an yi aurensu a Solwezi Civic Centre bayan kasaitattun abincin gargajiya da iyayen amaryar suka gabatar a bikin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hotunan auren masoyan sun bayyana a Facebook inda mai daukar hoto Edwin Mwanza Jr wanda aka fi sani da Mr Malaiti ya wallafa.

"Sun dauka rantsuwar aurensu kuma daga bisani aka yi liyafa da abokai, 'yan uwa da makusanta a otal din Ka san shi dake Solwezi," rahoton Nkani ya bayyana.

Abokan kusa na angon sun ce, an yanke shawarar yin shagalin cikarsu shekaru goma na tarayyarsu tare da shagalin zagayowar ranar haihuwar su duk a watan Nuwamba.

Ma'abota amfani da Facebook sun yi martani

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Birnin Katsina, Sun Halaka Rai Sun Sace Ma'aurata

Jama'a tuni suka fara tururuwar yin tsokaci tare da mika sakon taya murna ga masoyan junan da burinsu ya cika bayan dogon lokaci.

Wasu kuwa sun dinga dora laifi kan namijin ta yadda ya ja kafa har sai yanzu aka yi aure.

Helen Nazyechy Mwandila: "Shekaru 11 cikakku. Ina kokarin ganin sun birge ni, amma 'yar tawayen da ke jikina ba za ta bari ba. Koma dai yane, ina taya ku murna."
Koli Mazafa: "Ajiye diyar wani na tsawon shekara 11 ba tare da ka aureta ba? Hmmm gayu a'a, ina fatan ya biya sadaki cikakke."
MaRk Classic: "Hmmmm wadannan mutanen sun cancanci digirin digir ba satifiket din aure ba."
Chisengo Loloji: "Shekaru 11 suna soyayya da yara biyu ai babu matsala. Kawata 'yar Kenya dake shekarunta na 20 kuma tana da kannai biyu, sai makonni biyu da suka wuce sannan suka yi aure."

Bidiyo: Yadda Budurwa Ta Gwangwaje Saurayinta da Kyautar PS5 Sabo Dal

Kara karanta wannan

Hotuna: Kyawawan jaruman fim mata 3 da suka cafke zukatan zakarun Super Eagle, sun aure su

A wani labari na daban, wani matashi da burinsa shine ya mallaki PS5 ya cika bayan budurwarsa ta cika masa wannan burin a kwanakin nan.

Budurwa ta yi kokari inda har ta siya masa sabuwar na'urar wasan ta PS5 kuma ta bashi a lokacin da bai taba zato ko tsammani ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng