Hotuna: 'Dan Afrika ya kafa tarihin zama mutumin da yafi kowa hangamemen baki a duniya
- Domingo Jacquim 'dan asalin kasar Angola ta Afrika ya tabbata mutumin da yafi kowa katon baki a duniya baki daya
- Matashin mai shekaru 28 ya kafa wannan tarihin bayan fadin bakinsa ya kai inci shida da rabi cif a bude
- An gano cewa, yana iya saka gwangwanin lemu mai daukar 330ml kacokan a cikin bakinsa ba tare da ya takura ba
Wani 'dan Afrika ya kafa babban tarihi a duniya bayan ya tabbata mutumin da yafi kowa katon baki a duniya, African Report Files ta ruwaito.
Kamar yadda aka gano, mutumin 'dan asalin kasar Angola kuma hangamemen bakinsa yana daukan gwangwanin kacokan guda daya a bakinsa.
Tuni tarihin duniya ya yadda cewa,, Francisco Domingo Joaquim mai shekaru 28 ya bayyana a matsayin mutumin da yafi kowa katon.
Bakin matashin ya kai girman inci shida da rabi a bude, wangamemen bakin Jacquim na iya daukan gwangwanin lemu mai cin ruwan lemu 330ml baki daya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda Guiness Book of World Recoeds ya bayyana, a ta tsaye katon baki ne kuma a ta kwance kato ne.
An saka masa suna "Angolan Jaw of Awe" a kasarsa, hakan yasa yake godewa Ubangji kan wannan gano da yayi wanda ba kowa yake samu ba.
Mutum mafi muni a fadin duniya ya aura mata ta 3 (Hotuna)
A wani labari na daban, bahaushe yana cewa so gamon jini, tabbas hakan ya tabbata a kan wani mutum wanda ake cewa yafi kowa muni a duniya. Godfrey Baguma mai wasan bada dariya ne a kasar Uganda, kuma an fi saninsa da Ssebabi.
Mafi munin mutumin a fadin duniyar ya aura masoyiyarsa a matsayin mata ta uku a wani irin kasaitaccen biki mai cike da shagali.
An daura auren masoyan inda suka zama mata da miji. Babu shakka suna cike da farin ciki inda suka dinga daukar hotunan da suka karade kafafen sada zumuntar zamani.
Asali: Legit.ng