Alena Wicker: Yarinyar Mai Shekaru 13 Da Ta Samu Shiga Jami'a Don Karatun Likita
- Wata hazikar yarinya mai shekaru 13, Alena Wicker, ta samu shiga jami'ar Alabama a Amurka domin yin karatun likta
- Wicker ta ce tana da shekaru 12 ta kammala babban makarantar sakandare sannan bayan shekara guda ta samu gurbin karatu a jami'a
- Mahifiyarta Wciker, Daphne McQuarter, ta ce tun yarinyarta na karama ta gano cewa hazika ce kuma ta kan koyar da ita karatu a gida
Amurka- A ranar 30 ga watan Yuni, Alena Wicker, yarinyar mai shekaru 13 ta sanar cewa ta samu gurbin karatu a Jami'ar Alabama da ke Birmingham Heersink domon karatun likitanci.
Hakan na nufin ita ce mutum mafi karancin shekaru wacce ta samu shiga jami'ar ta Alabama don yin karatun likitanci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wicker ta samu gurbin karatun ne a shekara guda bayan ta kammala makarantar babban sakandare tana shekaru 12.
"Yau, ina gode wa Allah. Na kammala babban sakandare ina shekara 12 kuma gani bayan shekara daya na samu gurbin karatun likita ina shekara 13," ta rubuta a shafinta na Instgram.
A rubutun da ta yi mai ratsa zuciya, matashiyar ta mika godiya ga mahaifiyarta saboda taimakon da ta ke bata, tana mai cewa mahaifiyarta ne dalilin nasararta.
Mahaifiyar Wicker ta magantu
Da ta ke magana da Washington Post, Daphne McQuarter, mahaifiyar Wicker, ta ce ta lura yarta hazika ce tun tana karama.
"Alena yar baiwa ce. Ya nuna yadda ta ke yin abubuwa da cigabanta. Tana karanta manyan littafai," in ji ta.
Wicker, a yayin hirar da ta yi da jaridar ta tuna yadda wani yaro ke matsa mata har yasa ta ji bata son zuwa makaranta kafin daga bisani ta koma.
Yarinyar ta ce mahaifiyarta ta rika koyar da ita a gida kuma tana koyon darrusa na manyan ajijuwa don ta habbaka iliminta.
Hakan, a cewarta ya saukaka mata bayan ta koma makaranta.
Asali: Legit.ng