Bidiyo: Biri ya salla wanka soso da sabulu, ya naɗe jikinsa a tawul, ya cakare da gilashi

Bidiyo: Biri ya salla wanka soso da sabulu, ya naɗe jikinsa a tawul, ya cakare da gilashi

  • Wani bidiyon shahararren biri mai dabara ya bayyana inda ya salla wanka da sabulu tare da cakarewa tamkar mutum
  • A wani bidiyo da ke yawo, an ga birin yayi wanka soso da sabulu kuma ya nade jikinsa a tawul cike da kwarewa bayan ya kammala wankan
  • Ba a nan ya tsaya ba, ya cakare da gilashi inda ya karkace tamkar mutum, lamarin da ya janyo maganganu daga jama'a

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wani takaitaccen bidiyo wanda People's Daily suka wallafa a shafinsu na Facebook ya nuna lokacin da wani katon biri yayi wanka da kan shi kuma yake cin duniyar shi da tsinke.

Birin yayi amfani da ruwan wurin watsa shi inda ya game dukkan jikinsa yayin da wani mutum yake taimaka masa. Bayan wankan da birin yayi, ya yi kokarin tsane ruwan daga jikinsa inda yayi amfani da tawul.

Kara karanta wannan

Bana Wasa Da Jin Dadin Iyalina Ko Kadan Kuma Ina Shirin Rufe Kofa Da ta Hudu, Lakcara mai yara 18

Katon Biri
Bidiyo: Biri ya salla wanka soso da sabulu, ya naɗe jikinsa a tawul, ya cakare da gilashi. Hoto daga People's Daily
Asali: Facebook

Biri na yi wa kansa wanka

Yadda birin ya kula da tsaftar kansa cike da kwarewa ya kayatar da jama'a. Yadda yayi amfani da katon tawul din wurin nade jikinsa yasa aka dinga yaba masa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daga bisani, ya yi amfani da bakin gilashi na kare idanu daga hasken rana inda ya cakare sannan ya karkace aka kyasta masa hotuna da sakakkiyar fuskarsa. Mutane da yawa sun yaba da irin kyan da birin yayi kuma yadda yayi wa kansa wanka ya kayatar matukar.

Jama'a sun yi martani

A kalla mutane sama da 200,000 ne suka kalla bidiyon kuma dubbai suka yi tsokaci a yayin rubuta wannan rahoton.

Legit.ng ta tattaro muku wasu daga cikin tsokacin jama'a.

Bernice Rheaume yace: "Yafi wasu mutane."
Beverly Dawn Whatley yace: "Ya birge ni yadda yayi amfani da sabulu da kuma yadda ya more. Yana son ya ji yana kamshi mai kyau."

Kara karanta wannan

Bayan Shekaru 15, Ma’aikacin Banki Ya Nemi Mai Gyaran Takalmin Da Ya Taimakesa, Ya Bashi Tukwici

Zeljka Kopic tace: "Wayyo, abun sha'awa".
Amber Tiamzon yace: "Halitta mai kyau!!!"

Hotuna: Ango ya zabi doki matsayin babban abokinsa a aurensa, har amarci ya tafi da shi

A wani labari na daban, wani masoyin doki ya yanke hukuncin amfani da ingarman dokin da yafi kauna a matsayin babban abokinsa a ranar aurensa kuma har ya kai ga tafiya da shi cin amarci.

Paul Boyles mai shekaru 47 ya shirya yadda dokinsa ya taya shi karbar aure a ranar aurensa sa masoyiyarsa Kay mai shekaru 48.

A matsayin dokin na babban abokin, an sanya dokin mai suna Erik dan kunne tare da sirdi na musamman.

Asali: Legit.ng

Online view pixel