Bidiyon tsohon limamin Harami tsuke cikin kananan kaya a kan tsadajjen babur ya janyo cece-kuce
- Bidiyon tsohon limamin harami, Sheikh Adel al-Kalbani tsuke cikin kananan kaya a wani babur din zamani ya janyo cece-kuce
- An nadi bidiyon ne ta manhajar Snapchat wanda aka ga limamin cikin farin ciki a kan babur din a gefen titi yana cike da farin ciki
- Tuni dai bidiyon ya dinga tashe a Twitter inda wasu suka dinga caccakarsa kan irin shigar da yayi wacce suka ce ba ta kamala bace
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Bidiyon limamin babban masallacin Annabi, Sheikh Adel al-Kalbani yana kan babur din Harley Davidson sanye da kananan kaya ya janyo hankalin jama'a masu tarin yawa.
A bidiyon da aka nada a Snapchat, an ga al-Kalbani zaune a kan babur din a gefen titi inda yake sanye da riga dake dauke da tutar Amurka. Yana murmushi tare da farin ciki yayin da ake nadar bidiyon.
Tuni sunan tsohon limamin ya dinga yawo a Twitter inda yayi tashe tun bayan sakin bidiyon a soshiyal midiya a ranar Litinin, lamarin da ya janyo cece-kuce.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bidiyon da ya yadu na tsohon limamin ya janyo maganganu inda wasu ke tsokacin caccaka yayin da wasu ke kare shi, The Islamic Information ta ruwaito.
Wani ma'abocin amfani da Twitter yace al-Kalbani bai yi wani abun assha ba kuma yana da damar yin duk abinda ya so. Sai dai ya tabbatar da cewa Musulmai sun saba ganin Limamai a cikin shiga ta kamala ba irin wannan ba.
Wani ma'abocin amfani da Twitter ya caccaki al-Kalbani kan shigarsa wacce ta ci karo da gemun da ya tara kuma yace Limamin yayi nisa daga kamala.
Allah ya yiwa mai kula da masallacin Manzon Allah, Agha Habeeb Muhammad al-Afari, rasuwa
A wani labari na daban, Allah ya yiwa daya daga cikin wadanda suka dade suna yi wa Masallacin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi hidima, Agha Habeeb Muhammad al-Afari, rasuwa.
Marigayin shine kuma ke kula da dakin da kabarin Annabi Muhammad yake.
Muhammad al-Afari ya rasu ne a ranar Laraba, 13 ga watan Yuli, kamar yadda shafin Haramain Sharifain @hsharifain ya wallafa a Twitter.
Za a yi Sallah janaizarsa a masallacin Annabi a yau Laraba bayan sallar Magariba.
Asali: Legit.ng