Bantaba sanin ina da ciki ba: Budurwa mai shafaffen ciki ta haihu a bandaki
- Lucy Jones, mai aiki a jirgin sama, ta haifa yarinya mace a yayin da ta shiga bandaki sakamakon ciwon ciki da ya kama ta
- Budurwar mai shekaru 22 ta matukar firgita bayan ta ga kafar jinjira ta bayyana kuma tana neman gangarawa a bandaki
- Lucy ta jaddada cewa tana shan maganin hana daukar ciki kuma tana ganin al'adarta a cikin watannin
Wata mata mai shekaru 22 ta shiga matukar mamaki bayan ta haifa kyakyawar yarinya mace a yayin da ta shiga bandaki sakamakon ciwon cikin da bai kai ya kawo ba da ya kama ta.
Tana ganin al'adarta
Lucy Jones, mazauniyar Bristol dake Ingila, tace bata taba sanin tana dauke da juna biyu ba kuma tana tunanin tana ganin al'adarta ko a lokacin da ya kamata a ce tana dauke da cikin.
Kamar yadda New York Times ta ruwaito, matar ta sha mamaki bayan da ta shiga bandakin kuma ta ji kamar wani abu ya fado, tana dubawa ta ga kafafun jinjira yana gangarowa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A take ta kira masu taimakon gaggawa wadanda suka iso tare da shan mamakin yadda lamarin ya faru.
Lucy ta ce: "Ban taba sanin ina da ciki ba har sai da na ga jinjirata a bandaki."
Lucy tace ta fuskanci ciwon ciki a baya kuma ta yi fama da ciwon ciki a daren jajiberin da zata haihu. Ta sake bayyana cewa, tana amfani da kwayoyin hana daukar ciki.
Budurwa ta haifo yaro ba tare da kwanciya da namiji ba, ta yi bayani dalla-dalla
A wani labari na daban, wata mata mai suna Aba tayi ikirarin cewa ta dauka ciki kuma ta haihu ba tare da ta sadu da namiji ba.
Yayin zantawa da Barima Kaakyire Agyemang a step 1 TV, Aba tayi ikirarin cewa shekara hudu rabonta da kwanciya da namiji.
Kamar yadda tace, lokacin da ta fara fuskantar wani irin ciwon ciki da kumburi, tace tayi tunanin cutar fibroid ce.
Bayan isarta asibiti, tayi ikirarin cewa an sanar da ita ta shirya za a yi mata aiki domin cire abinda ke cikinta, shafin Linda Ikeji ya rahoto.
Ta kara da cewa, ta yi kokarin yin mishi domin cutar fibroid din ta fita ba tare da an tsaga ta da wukar likita ba, amma abun mamaki sai santalelen yaro namiji ya fado.
Asali: Legit.ng