Dadin duniya: Jerin kasashen duniya 23 mafi farin ciki da rayuwa mai dadi
- Kowace kasa a duniya na da yadda mazauna cikinta ke rayuwa, ko dai cikin tsananin kunci, farin ciki ko tsaka-tsaki
- Wani rahoto ya yi waiwayen jerin kasashe mafi farin ciki a duniya, kuma a jeren babu kasar Afrika ko daya cikin 19
- A shekarar da ta gabata, Najeriya ta fito cikin kasashen Afrika mafi farin ciki, inda ta fito a matsayin kasa ta 17
Rahoton farin ciki na duniya, bugun wata cibiya a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana kusan kasashe 150 da suka fito a jerin kasashen da ake walwala da farin ciki a duniya.
Da yake cika shekaru 10 na aikin tattara bayanan, rahoton yana nuna yanayin rayuwa a kasashen duniya - kasashen da ke cikin farin ciki, wadanda suke cikin kunci da ma wadanda ke tsaka-tsaki, da kuma dalilan da ke jawo yanayin kowace kasa.
A rahoton da muka tattara, an bayyana jerin kasashe 19 da suka fi rayuwar farin ciki a duniya kamar yadda yazo a rahoton worldhappiness.report.
Ga jerin kasashen
1. Finland
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
2. Denmark
3. Iceland
4. Switzerland
5. Netherlands
6. Luxembourg
7. Sweden
8. Norway
9. Isra'ila
10. New Zealand
11. Austria
12. Australiya
13. Ireland
14. Jamus
15. Kanada
16. Amurka
17. United Kingdom
18. Czechia (Czech Republic)
19. Belgium
20. France
21. Bahrain
22. Slovenia
23. Costa Rica
Manyan kasashe 17 mafi farin ciki a Afirka a 2021, Najeriya ce ta karshe
A wani labarin na daban, rahoton farin ciki na duniya na 2021 ya tantance kasashe bisa la’akari da yadda suke farin ciki.
Rahoton wanda Kungiyar Hadin Gwiwar Cigaba ta Majalisar Dinkin Duniya ta wallafa ya nuna kasar Finland a matsayin kasa mafi farin ciki a duniya.
Ya duba yadda cutar COVID-19 ta shafi tasirin mutane da jin daɗin su da kuma sakamakon da rufe kasashe ya haifar.
Asali: Legit.ng