'Dan uwan ango ya bindige amarya ana tsaka da shagalin biki, ta sheka lahira
- 'Dan uwna ango mai shekaru 36 ya bindige amarya ana tsaka da shagalin bikinsu a birnin Firuzabad dake kasar Iran
- An gano cewa, 'dan uwan angon ya harba bindigar ne duk a cikin murna amma aka yi rashin sa'a bai iya sarrafata ba kuma bashi da lasisi
- A take harsashi ya bula kwakwalwar amaryar wacce ta fadi sannan daga bisani tace ga garinku, wasu mutum 2 sun jigata a wurin
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Ana tsaka da shagalin biki, an bindige amarya yayin da 'dan biki ya harba bindiga duk a cikin murna kuma ya sameta a kan ta.
Mahvash Leghaei mai shekaru 24 tayi aure a Firuzabad a Iran yayin da 'dan biki wanda ya kasance 'dan uwan ango ne, ya harba bindigarsa mara lasisi wacce yake amfani da ita wurin farauta.
An gano cewa, kai tsaye harsashin ya shiga kan mata kuma ya jigata 'yan biki maza har su biyu.
Kakakin rundunar 'yan sanda, Kanal Mehdi Jokar yace: "An yi mana kiran gaggawa kan harbin da aka yi a wurin shagalin biki a birnin Firuzabada kuma a take muka aika jami'ai.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Jami'an sun gano cewa wani ne ya harba bindigarsa ta farauta a matsayin wani bangare na al'adarsu, amma cike da takaici sai ya samu amarya a kai da wasu maza biyu saboda bai iya sarrafa bindigar ba.
"Mai harbin ya bar yankin amma 'yan sanda sun cafko shi yayin da yake dauke da bindigar farautan mara lasisi wacce yayi harbin da ita."
Kamar yadda rahotannin farko suka bayyana, ya saki harsashin farko kuma babu abinda ya faru, na biyun ne ya samu amarya ya ratsa kwakwalwarta kuma ya shafi wasu baki biyu, New York Post ta ruwaito
Zargin cin amana: Hotunan magidanci da ya sheke matarsa, ya mika kansa hannun 'yan sanda da muhimmiyar shaida
Kakakin rundunar 'yan sandan yace da farko amarya ta fadi a sume amma daga baya ta rasu, sai dai mutum biyun da harsashin ya shafa sun samu rauni amma ba mai yawa ba.
Mirror.co.UK ta ruwaito cewa, wanda yayi harbin an gano shekarunsa 36 da haihuwa kuma 'dan uwan angon ne.
Kakakin rundunar 'yan sandan ya kara da cewa: "Duk wani tada zaune tsaye irin haka 'yan sanda sun hana kuma suna daukar mataki, akwai bukatar mutane su san hakan kuma da haramcin harbi a wurin biki.
"Zamu dauka mummunan mataki kan duk wanda muka kama yana karya wannan dokar."
'Yan uwan amaryar sun ce sun bada kyautar sauran sassan jikinta kuma sun taimaki mutum uku da shi.
Al'adar harba bindiga a bukukuwa haramun ne a dokokin kasashe amma har yanzu ana yin hakan a gabas ta tsakiya.
Asali: Legit.ng