Wani mutum ya nadi bidiyon matar makwabcinsa da ta kai kwarto daki, tana kokarin fitar dashi
- Wani mutum ya nadi bidiyon yadda matar makwabcinsa take ta kokarin fitar da kwarton da ta kai dakinta bayan sun kammala abinda zasu yi
- A bidiyon, an ga kwarton hankali tashe inda duk ya rude yana kokarin tsallakawa ya dire, gudun tonuwar asirinsa
- A daya bangaren, matar ta bayyana a rikice yayin da take kai wa da kawowa domin duba ko mijinta ya iso, ko kuma kwarton nata ya dire ya arce
Wani mutum ya nadi bidiyon matar makwabcinsa yayin da ta gama shagalinta da kwartonta kuma tana son fitar da shi daga gidan.
Makwabcin wanda ya ga abinda ya faru kuma ya yanke hukuncin nadar lamarin a wayarsa daga dakinsa, ya bayyana irin cin amanar da matar tayi wa mijin ta.
Ma'auratan suna zama ne a rukunin gidaje wanda ke dauke da dakunan mutane da yawa, hakan ne yasa fitar kwarton matar ya nemi ya basu wuya.
Idan yace zai diro shine kawai hanyar da zai fita cikin sauki, amma kuma kwarton ya bayyana a rude kuma tsoro ya bayyana a fuskarsa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya dinga yunkurin dira kasa amma ya dinga sauya wurin dirar inda ita kuwa matar auren ta dinga kai wa tana kawowa tare da duba ko mijinta ya shigo gidan.
Ta bayyana a tsorace tare da rikicewa yayin da take ta kokarin ganin kwarton ta ya fice daga gidan don asirinta ya rufu.
Zargin cin amana: Hotunan magidanci da ya sheke matarsa, ya mika kansa hannun 'yan sanda da muhimmiyar shaida
A wani labari na daban, magidanci mai shekaru 55 ya sheke matarsa mai shekaru 45 bayan ya zargeta da cin amanarsa kuma daga bisani yayi tafiyar kusan kilomita 12 zuwa ofishin 'yan sanda da kanta.
Lamarin ya faru ne a Chandrasekharpur dake yankin Odisha Dhenkanal a sa'o'in farko na ranar Juma'a, 15 ga watan Yulin 2022.
Bidiyon mai matukar ban tsoro na mutumin yana tafe da kan matarsa da ya sheke ya yadu a kafafen sada zumuntar zamani.
'Yan sanda sun kama wanda ake zargin yayin da yake tafe da cirarren kanta zuwa ofishin 'yan sanda dake yankin Dhenkanal.
Asali: Legit.ng