Bidiyo: Mazaunan roban da budurwa ta saka sun fadi tana tsaka da rawa a fili

Bidiyo: Mazaunan roban da budurwa ta saka sun fadi tana tsaka da rawa a fili

  • Wata zukekiyar budurwa kuma 'yar kwalisa ta sha matukar kunya bayan mazaunan roba da ta saka sun zazzage ana tsaka da rawa
  • Budurwar mai cike da diri, sura da tsari tun farko ta bayyana a matsayin 'yar kwalisa inda ta hau fagen rawa tare da wani matashi
  • Sai dai cike da mamaki aka ga mazaunanta suna zazzagewa yayin da rawa yayi rawa, an gano cewa surar ta bogi ce ba mallakinta ba

Wata zukekiyar budurwa a cikin kwanakin nan ta bai wa jama'a ma'abota amfani da soshiyal midiya dariya bayan bidiyonta ya yadu.

Bidiyon budurwa da ya bayyana ya nuna 'yar kwalisan a fagen rawa inda ta ci gayu iyakar iyawarta tare da wani matashi.

Diri, tsari da surar budurwar ya matukar kayatar da jama'a da farko kafin fallasar boyayyen sirrinta.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Daga zuwa yawon sallah, ta dawo ta tarar da gidanta tare da motarta kurmus

Fake Nyansh
Bidiyo: Mazaunan roban da budurwa ta saka sun fadi tana tsaka da rawa a fili. Hoto daga dailymail.co.uk
Asali: UGC

Ana tsaka da rawa kwatsam aka fara ganin sauyin ba-zata a bangaren mazaunanta, ashe mazaunan roba ta saka inda ta fito cas.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A bidiyon da jaridar Daily Mail ta wallafa, an ga yadda masoya maza da mata suke rawa a fagen cike da shauki tare da soyayya.

Ta yuwu budurwar bata san abinda ka iya zuwa ya dawo ba, shiyasa ta zage ta dinga kwasar rawanta ba tare da tayi tunanin cikon da ke mazaunanta zasu iya zazzagewa ba.

Kalla bidiyon a nan.

Magidanci ya cinye akuya 1, 2Kg na shinkafa da donot 40 a zama daya, matarsa ta tsere

A wani labari na daban, wani mutum 'dan kasar Tanzania ya iya cinye 2kg na shinkafa da akuya daya a zama daya. Ya sanar da cewa matarsa ta gudu ta bar shi saboda tsabar cin abincinsa.

Kara karanta wannan

Idan da mai bukata, a neme ni: Bidiyon dirarriyar BaAmurkiya da tace 'dan Najeriya take son aure

Msosi ya yi nasarar lashe gasar cin abinci ta Tonge nyama. Saidi Msosi, wanda yayi nasarar lashe gasar cin abinci ta Tonge nyama a Morogoro, ya bar mutane baki bude saboda yadda ya cinye donot 40 a cikin minti 20 kacal.

A wata tattaunawa da Millard Ago, Msosi yace ya ziyarci likita kuma an sanar masa cewa hana da katon ciki ba kamar na sauran mutane ba kuma ya cigaba da cin abincinsa.

"Na cinye donot 40 a cikin minti 20 kacal. Na fara cin kwano uku zuwa hudu har na kai ga mataki babba," Msosi yace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng