Ci gaba: Dangote ya sake banke mutum 20, ya zama na 63 a jerin masu kudin duniya
- Dan Najeriya kuma mafi dukiya a Afrika ya sake tsallake matsayi mai girma a jerin attajiran duniya na Bloomberg
- Wannan na zuwa ne kasa da mako guda da Dangote ya tsallake wani matsayin mai ban mamaki a jerin
- Rahoton da muka samo ya bayyana irin karin arzikin da Dangote ya samu har ya zama na 63 a duniya a yanzu
New York, Amurka - Attajirin Najeriya Aliko Dangote ya zama na 63 a jerin attajirai a duniya, kamar yadda wani sabon jadawali na Bloomberg ya nuna.
A cikin kididdigar da aka fitar jiya, shugaban Tesla, Elon Musk, ya fito a matsayin attajirin da ya fi kowa kudi a duniya har ila yau, rahoton Vanguard.
Dangote, wanda ya haura matsayi 37 a jerin attajiran Bloomberg na baya-bayan nan, ya tara dala biliyan 20.2 ya zuwa ranar Litinin, 13 ga Yuli, 2022.
Ya kasance a matsayin mutum na 65 mafi arziki a duniya a ranar Juma'a 8 ga Yuli, 2022, kamar yadda rahoton mu na baya ya kawo.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kididdigar biliniyoyi na Bloomberg wani kididdiga ne da ke auna kimar dukiyar attajiar a yau da kullum duba da tafiyar kasuwar hannayen jari.
Hakazalika, a kowace rana sabunta kiddigar ake kamar yadda kafar ta fada a wani rubutu da ta yi a baya-bayan nan
A cewar Bloomberg, kamar yadda Leadership ta kawo:
"An ba da cikakkun bayanai game da adadin na kididdigar ne da aka samo daga shafin bayanai na biliniyoyin. Ana kuma sabunta alkalumman a karshen kowace rana a New York."
Mu dawo ga Dangote, wanda ya fi kowa arziki a Afirka, sananne cewa yana kula da masana'antar Dangote, wacce ke samar da kusan komai na abubuwan rayuwar yau da kullum.
Dangote ya mallaki 85% cikin 100% na masana'antar simintin Dangote da ke hannun jarin jama'a da dama.
Arzikin nufin Allah: Kudi sun karu, Dangote ya zama na 65 a jerin masu kudin duniya
A makon jiya, Aliko Dangote, shugaban rukunin Dangote, ya tsallake matsayi 35 a jerin attajiran duniya na Bloomberg, daya daga cikin manyan attajirai 100 a duniya.
Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, a cewar Bloomberg, yana da dala biliyan 20.4 kamar yadda a ranar Juma'a 8 ga Yuli, 2022, kuma hakan ne ya kai shi ga matsayi na 65 a mafi arziki a duniya.
Rahoton ya kuma nuna cewa daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa Yuli, Dangote ya samu dala biliyan 1.30, wanda hakan ya taimaka masa wajen barin matsayi na 100 da yake a farkon 2022.
Asali: Legit.ng