Bidiyo: Yadda ake rayuwa a cikin gidan gurgu magidanci mai mata 17 da 'ya'ya 84
- Bidiyon magidancin gurgu mai matan aure 17 da 'ya'ya 84 dake zama a birnin Dubai dake UAE ya ba jama'a da yawa mamaki
- Dattijon magidancin duk da gurgu ne yana yawo da sanda, ya mallaki tafkeken gida inda akwai sashi daban-daban
- Alamu na nuna cewa bai gama haihuwa ba tunda har a bidiyon an bayyana wasu yaran goye da kuma wasu kananan da zasu kai takwas
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Bidiyon wani magidancin gurgu mai mata 17 da 'ya'ya 84 a birnin Dubai dake hadaddiyar daular Larabawa ya ba jama'a masu yawa mamaki da al'ajabi.
Kamar yadda bidiyon mai dauke da yadda gidansa da yadda rayuwar gidan ke gudana ya nuna, yara ne gare shi wadanda ya haifa da mata 17 har su 84.
A bidiyon da mai wasan barkwanci LaVar Walker ya wallafa a shafinsa na Facebook, magidancin ya bayyana wasu daga cikin 'ya'yansa masu shekaru da ba zasu wuce bakwai zuwa daya ba har su takwas.
Ya bayyana cewa, ya rasa kafafunsa tun shekarar 1999 kuma ya zagaya cikin gidan inda aka nadi bidiyon yadda yake.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Gidan na dauke da sashinsa na mai gida inda yake da tafkeken dakin bacci da gadajensa har biyu, a bayyane yake cewa bangaren matansa da 'ya'yan daban yake da nashi.
A wani bangare na gidan kuwa, an hango wasu daga cikin 'ya;yansa suna ta wasanninsu da motar yara inda wasu ke tura wasu.
A can daya bangare kuwa, wasu daga cikin matan ne ke zaune yayin da wasu ke tsaye duk sanye da bakaken riguna inda suka lullube kawunsu.
Ko a yayin rubuta wannan rahoton, mutum dubu 15 ne suka yi martani a bidiyon yayin da wasy miliyan 8 suka kalla.
Martanin jama'a
Legit.ng ta tattao muku wasu daga cikin martanin jama'a
Jama Abdillahi Biime yace: "Ya birgeni yadda yayi dariya yayin da 'dan jaridar yace masa shu matarsa daya."
Adonis Mel yace: "Na tausayawa yaran, ba wai samar da abincu bane kawai, ba zaka iya gina alaka da mahaifinka ba bayan kana da 'yan uwa 83. Kai, ba dole ma ya dinga iya tuna sunayen dukkansu ba. Kai wannan abu yayi yawa."
Cora Gorge cewa tayi: "A gaskiya gara kada in yi aure da dai in hada miji da wata."
Asali: Legit.ng