Firaministan Birtaniya Boris Johnson zai yi murabus daga shugabancin jam’iyyar sa
- Ana san ran Firaministan Birtaniya Boris Johnson zai sauka daga mukamin na shugaban jam'iyar conservatives a yammacin yau Alhamis
- Duk da cewa Boris Johnson bai kammala yin murabus ɗin ba a hukumance, an fara kamfe kan wanda zai gaje shi.
- Mista Johnson zai cigaba da zama firaministan kasar har zuwa watan Oktoba kafin a nada wanda zai maye gurbin sa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Ingila - A Yau Alhamis ne Firaministan Birtaniya Mista, Boris Johnson zai sauka daga mukamin shugabancin jam’iyyar ta Conservatives. Rahoton BBC HAUSA
Mista Johnson zai cigaba da zama firaministan kasar har zuwa watan Oktoba.Yanzu za a nada sabon shuagaban jam’iyyar Conservative da zai maye gurbin sa, sannan a zabi sabon Firaminista a watan Oktoba
Har an fara yin kamfen din wanda zai gaji Boris duk da cewa bai kammala yin murabus din ba a hukumance.
Firaminista Boris Johnson zai bayyana yin murabus din nasa ne zuwa anjima, yau ranar Alhamis
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Mai Magana da yawun fadar gidan gwamantin Ingila Mai Lamba 10 Darwin street ya ce: "Firaministan zai yi sanarwa ga ƴan ƙasar zuwa an ji ma."
Firaminista Boris Johnson ya yi magana ne da Sir Graham Brady, shugaban kwamitin jam'iyyar Conservative na 1922 , inda ya sanar da shi matakin da ya ɗauka, inji majiyar.
Majiyar ta ƙara da cewa: "Mista Boris Johnson ya yi magana da Graham Brady inda ya amince ya sauka a kan lokaci don ba da damar naɗa wani sabon shugaban a Oktoba."
Ma’aikata sun batar da fasfon Bayin Allah, maniyyata ba za su yi aikin Hajjin bana ba
Ghana - A kasar Ghana, an jefa masu niyyar yin aikin hajjin wannan shekara a tsaka mai wuya, domin an nemi takardunsu, duk an rasa.
Wani labari mara dadi da ya fito daga VOA Hausa, ya bayyana cewa akalla maniyyata 176 ne aka rasa inda takardun fasfonsu suka shiga.
Asali: Legit.ng