Jirgin sama ɗauke da mutane sama da 100 ya kama da wuta a kasar Amurka
- Wani Jirgin sama da ya samu matsala yayin sauka ya kama da wuta a filin Jiragen sama na birnin Miami da ke ƙasar Amurka
- Wani bidiyo ya nuna yadda Fasinjojin cikin jirgin ke ihun neman taimaki yayin da suke rige-rigen fitowa daga cikin jirgin saman
- Wani rahoto ya bayyana cewa jirgin ya bugi wasu gine-gine biyu kafin ya tsaya a cikin ciyayi
Aƙalla mutum uku suka jikkata aka kwantar da su a Asibiti bayan wani jrigin sama ya kama da wuta jim kaɗan bayan ya sauka a filin sauka da tashin Jiragen sama na Miami, ƙasar Amurka ranar Talata.
Daily Trust ta ruwaito cewa hukumar kashe Gobara ta birnin Miami ta ce Jirgin na ɗauke da Fasinjoji 126 da kuma ma'aikata 11 yayin da lamarin ya faru.
Wani Bidiyo da aka watsa a kafar Intanet ya nuna yadda Fasinjojin ke ihu yayin da suke turereniyar fita daga Jirgin mai ci da wuta don tsira da rayuwar su.
A ruwayar wata ƙafar watsa labarai WSVN, ta tattara rahoton cewa Jirgin saman mallakin kamfanin sufurin jiragen sama na Red Air ya dira ƙasa ne da misalin ƙarfe 5:30 na yamma.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Rahoton ya ƙara da cewa Jirgin ya taso ne daga Jamhuriyar Dominican kuma yayin saukarsa a filin ya bugi wani ginin Hasumiya ta sadarwa.
Haka nan kuma yayin saukar ya taɓa wani ƙaramin gini kafin ya tsaya a wani fili mai ciyayi da ke gefen hanyar da jirage ke gudu kafin tashi.
Me ya hadda wannan hatsari?
Bayanai sun nuna cewa giyar saukar Jirgin ce ta samu matsala har ta kai ga ta daina aiki sam yayin da matuƙan jirgin ke kokarin saukar da shi.
Wasu sassan hasumiyar sadarwa da jirgin ya buga kafin sauka sun maƙale a fukafukan jirgin kuma ana iya ganinsu a cikin Bidiyon.
"Zamu kasance a filin jiragen saman ranar Laraba," a cewar hukumar sufuri ta ƙasar Amurka.
A wani labarin kuma Bayan tafiyar Peter Obi, Gwamnan Bauchi da wani Jigon PDP sun dira gidan Wike, sun sa labule
Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi da Mataimakin shugaban APC na shiyyar kudu maso kudu, Chief Dan Orbih, yanzu haka sun shiga ganawar sirri da gwamnan Ribas, Nyesom Wike.
Babban mai taimaka wa gwamnan Bauchi ta ɓangaren Midiya, Kelvin Ebiri, shi ya tabbatar da haka ga jaridar Leadership a Patakwal, babban birnin Ribas.
Asali: Legit.ng