Wata Kasar Afirka Ta Sha Gaban Najeriya a Matsayin Kasa Da Ke Kan Gaba Wajen Hako Danyen Mai a Afirka

Wata Kasar Afirka Ta Sha Gaban Najeriya a Matsayin Kasa Da Ke Kan Gaba Wajen Hako Danyen Mai a Afirka

  • A lokacin da farashin danyen man fetur a kasuwanin duniya ya kai $120 duk ganga, an samu ragowar man da Najeriya ke fitarwa
  • Alkalluman baya-bayan nan sun nuna cewa wannan shekarar ne mafi muni ga Najeriya hakan yasa ba za ta amfana daga ciniki ba a lokacin da kasashen turai ke neman mai
  • Sakamakon matsalar da Najeriya ke samu wurin samar da danyen man fetur, Angola ta wuce Najeriya ta zama itace kan gaba wurin samar da mai a Afirka

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

A halin yanzu ba Najeriya bace kasa da ke kan gaba wurin samar da mai a Afirka a watan Mayu saboda raguwa da ta samu a yayin da ake sayar da gangan mai a $121.33.

Kamar yadda alkallumar da aka samu daga kungiyar kasashe masu fitar da man fetur, OPEC, ta wallafa, man da Najeriya ke fitarwa ya ragu da ganga 195,000 duk rana zuwa 1.02 miliyan a Mayu daga 1.22 miliyan a watan Afrilun 2022.

Kara karanta wannan

Daga zuwa biki: 'Yan bindiga na neman fansan N145m kan bakin bikin Zamfara

Man da Angola ke fitarwa shima ya ragu, amma tana fitar da ganga 1.6 miliyan duk rana, hakan na nuna cewa ta fi Najeriya.

Rahoton OPEC na kasashe masu hako man fetur a duniya.
Angola Ta Doke Najeriya a Matsayin Kasa Da Ke Kan Gaba Wajen Hako Danyen Mai a Afirka. Hoto: OPEC.
Asali: Original

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani sashi na rahoton na OPEC ya ce:

"Danyen man fetur da Saudiya da UAE da Kuwait ke samarwa ya karu, yayin da ya ragu a Libya, Najeriya, Iraq, Gabon da Iran.
"Alkalluman farko sun nuna cewa dan man fetur da ake samarwa a duniya zai ragu a Mayu da ganga 0.15 miliyan a kowanne rana idan aka kwatanta da 98.75 miliyan da ake samarwa a watan da ta gabata."

Tsadar man fetur: Najeriya na da mai sama da lita 1.9bn a boye, ministan Buhari

A wani rahoton, Timipre Sylva, Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur ya bayyana cewa yanzu haka Najeriya na da lita biliyan 1.9 na man fetur a ajiye.

Kara karanta wannan

An Kori Lakcarorin Najeriya 2 Saboda Tafka 'Manyan' Laifuka a Jami'a

A cewarsa, wannan mai na iya gamsar da bukatun kasar na tsawon kwanaki 32, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Ministan ya bayyana haka ne jiya Laraba 9 ga watan Maris a Abuja yayin da yake magana a gaban majalisar zartarwa ta tarayya a zaman da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: