Kullu nafsin: Bayan shekaru 70 yana sallah a bayan limamin Ka'aba, Allah ya karbi rayuwarsa
- Allah ya yiwa Sheikh Muhammad bin Abdul-Wahhab Aal Ash-Sheikh, attijon da ya shafe tsawon shekaru 70 yana sallah a bayan limaman Masallacin Ka’aba rasuwa
- Sheikh Muhammad ya amsa kiran mahaliccinsa ne a ranar Laraba, 25 ga watan Mayu, a wani asibitin Jiddah
- Marigayin ya yi sallah a bayan Limaman Masallaci mai tsarki da dama kuma yana yawan bayyana a bidiyo tsaye a bayansu
Saudiyya - Dattijon da ya shafe tsawon shekaru 70 yana sallah a bayan limaman Masallacin Ka’aba, Sheikh Muhammad bin Abdul-Wahhab Aal Ash-Sheikh, ya kwanta dama.
Sashin Hausa na BBC ya ruwaito cewa Sheikh Muhammad ya rasu ne a ranar Laraba, 25 ga watan Mayu, a wani asibiti da ke Jiddah, babbar birnin kasar Saudiyya.
Marigayin ya kasance daga cikin mutanen da suka samu falalar yin sallah a bayan limaman Masallacin Harami, ya kuma shafe tsawon shekaru 70 a wannan matsayin.
Ana yawan ganinsa a bidiyo a bayan limaman a cikin shekara 10 da suka wuce.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sunaye, hotuna da bidiyoyin kira'ar limamai 6 na Masallacin Annabi da ke Madina
A wani labari na daban, ba tare da tantama ba, zama limamin masallacin Annabi shi ne abu mafi girma, karramawa da alfahari a duniyar Musulunci baki daya. Ba kowa Allah madaukakin Sarki ke bai wa irin wannan damar da karamar ba.
Duk da gwamnatin Saudi Arabiya ce ke nada limamai, dole ne a cike wadannan ka'idojin hudu kafin zama limamin masallacin Annabi, kamar yadda Argaam suka ruwaito.
- Kasancewar mutum mazaunin kasar Saudi na dindindin.
- Kaiwa shekaru 30 ko sama da haka.
- Mallakar digiri a fannin shari'a daga wata jami'ar Saudi.
- Haddace Qur'ani da kira'a mai dadi.
Asali: Legit.ng