Mi'ara Koma Baya: Birtaniya Ta Ayyana Mambobin Ƙungiyar IPOB a Matsayin Ƴan Ta'adda
- Gwamnatin Birtaniya ta ayyana kungiyar masu fafutikan kafa kasar Biafra wato IPOB a matsayin kungiyar ta'addanci
- Sanarwar ta Birtaniya na kunshe ne cikin sabbin dokokinta na bada mafaka ga mutanen da ke kungiyar IPOB, MASSOB ko wata kungiya mai alaka da Biafra
- A cewar sabbin ka'idojin, kungiyar ta IPOB da sashin mayakanta na Eastern Security Network, ESN, suna da hannu kan ayyukan keta mutuncin dan adam a Najeriya
An haramta wa yan kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB), da Movement for the Actualisation of Sovereign State of Biafra (MASSOB) da sauran kungiyoyin Biafra samun takardar izinin samun mafaka a Birtaniya.
The Punch ta rahoto cewa gwamnatin na Birtaniya, a sabbin dokokinta da aka wallafa a shafinta na intanet a ranar 3 ga watan Mayu, ya ce IPOB, da gwamnatin Najeriya ta ayyana a matsayin kungiyar ta'addanci, da ESN, sun aikata laifukan keta mutuncin bil-adama.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A sanarwar mai kasar ta Birtaniya ta fitar, ta ce Hukumar shiga da fice na kasar ba za ta bada mafaka ba ga mutanen da suka aikata laifukan cin zarafin bil adama.
A watan Maris na shekarar 2021, gwamnatin na Birtaniya cikin shawarwarinta ta bukaci mahukunta su duba yiwuwar bawa mambobin IPOB mafaka.
Shawarwarin da aka bawa mahukunta game da masu neman mafaka
Dokokin sun ce akwai yiwuwar duk wani dan kungiyar ko wanda ke goyon bayan kungiyar ya fuskanci barazanar kamu, tsarewa ko rashin kyautatawa wanda ya zai iya zama kuntatawa.
Amma, a sabbin dokokinta, kasar ta Birtaniya ta amince cewa sashin mayaka na kungiyar da aka kirkira a Disambar 2020 an rahoto sun aikata laifukan cin zarafin dan adam.
Sabuwar dokar ta ce:
"An haramtawa MASSOB amma ba a ayyana ta a matsayin kungiyar ta'addanci ba a Najeriya. Ita ma an rahoto ta yi rikici da dama da hukumomin gwamnati.
"Duk wani da aka samu yana da alaka da IPOB, MASSOB ko wata kungiyar 'Biafra' da ke amfani da rikici don cimma manufar ta, ya zama dole mahukunta su duba ko dokar haramtawa masu neman mafaka zai yi aiki a kansu."
Saurari karin bayani ...
Asali: Legit.ng