Rai mai alkawari: Ana dab da jefa tsoho a ma'adanar gawawwaki, an gano da ransa bai mutu ba
- An kusa kai wani dattijo dan kasar China, mai suna Jeffrey Mensah ma'adanar gawawwaki bayan an yi kuskuren sanar da mutuwarsa
- An sanya wa mutumin likkafini, tare da aje shi cikin makara, yayin da ma'aikatan ma'adanar gawawwakin suka yi mamakin gano cewa yana da ransa lokacin da suke kokarin ajiye shi
- Hankalin masu amfani da yanar gizo ya matukar tashi, duba da yadda aka kusa birne mutumin da a ce ba a gano yana da rai ba
An kusa birne wani dattijo mazaunin Shanghai da ransa, bayan an yi zaton ya mutu, inda aka kai shi ma'adanar gawawwakin a likkafini a babban birnin da cutar Korona tayi kamari, yayin da miliyoyin mutane ke cikin kullen gwamnati.
CNN sun ruwaito bidiyon yadda wani da ke tsaye a wurin ya dauka, wanda ke nuna ma'aikatan da ke sanye da takunkumin kariyar gaba daya jiki, yayin da suka gane cewa mutumin na da rai.
Bidiyon da aka wallafa a ranar Lahadi na nuna kan mutumin daga rigar gawa mai kalan dorawa inda ma'akatan suka dauko gawar daga mota.
Za a iya jiyo muryar wanda ya dauki bidiyon, daga wani gini kusa da wurin yana cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Asibiti yanzu ya zama shirme. Suna sanar da rayayyun mutane a matsayin mattatu. Ma'aikatan ma'adanar gawawwakin sun ce suna da ransu. Hakan bai kyautu ba."
Masu amfani da yanar gizo sun fusata a Weibo, wani shafi mai kama da Twitter na kasar China. Mutane da dama basu yarda irin wannan babban kuskuren zai iya faruwa ba.
Wani ya yi tsokaci: "Wannan karon matsalolin Shanghai sun bayyana karara,"
Wani ya rubuta: "Wannan yana nuni da kashe mutanen fadin duniya da ganganci."
An tsinta gawar magidanci da budurwa a mota, sun mutu suna tsaka da 'kece-raini'
A wani labari na daban, an tsinta gawar wani mutum da wata mata wadanda aka gano sun mutu a cikin mota kirar SUV yayin da suke tsaka da jima'i.
The Nation ta ruwaito cewa, an tsinta gawarsu a daren Lahadi a rukunin gidaje na Jakande da ke Isolo a jihar Legas yayin da makwabta da suka balle motar bayan sun lura da injinta a kunne tun daga ranar Asabar.
Mutumin mai suna Koyejo ya dauka masoyiyarsa wacce ba a san sunanta ba yayin da yake hanyarsa ta zuwa gidan iyayensa da ke rukunin gidaje na Jakande a Isolo kamar yadda abokansa suka yi ikirari.
Asali: Legit.ng