Yadda mace bakar fata ta ciyar da dubban mabukata na tsawon shekaru 40

Yadda mace bakar fata ta ciyar da dubban mabukata na tsawon shekaru 40

  • Janet Easley, mai zama a cikin birnin Indiana, ta dauki tsawon shekaru 40 tana ciyar da marasa galihu da fursunoni masu tarin yawa
  • Matar mai zuciyar taimako ta ciyar da mutane dubu goma a shekarar 2018, sannan tana cigaba da irin wannan karamcin duk shekara
  • Easley ta ce babu abunda zai canza a shekara mai zuwa, saboda ta tsara kaiwa, gami da ciyar da mutanen da suka fi wandanda take ciyarwa a baya

Janet Easley mai matukar kirki ta dauka tsawon lokaci tana bia wa dubbannin marasa karfi da gajiyayyu abincin dare a tsakiyar Indiana duk lokacin hutu na tsawon shekaru 38.

Janet Easley ta tarbi duk wanda ya halarci shirin ciyar da abincin dare na iyalin Turner, wanda ake gudanarwa a wuraren uku na birinin Indiana.

Kara karanta wannan

Sokoto: Bishop Kukah ya yi martani kan kashe dalibar da ta yi batanci ga Annabi

Yadda mace bakar fata ta ciyar da dubban mabukata na tsawon shekaru 40
Yadda mace bakar fata ta ciyar da dubban mabukata na tsawon shekaru 40. Hoto daga @hammariethomas
Asali: Twitter

Easley ta gayyaci kowa duk da yara da iyaye, musamman iyayen marayu dake cikin tsananin rayuwa.

Ba Easley kadai ke gudanar da shirin tallafin ba; tana samun tallafi daga wasu mutane 200, tare da 'yan gidan yarin mata dake dafa talotalo.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Matar ta ciyar da kusan mutane dubu goma a shekarar da ta gabata, sannan tana sa ran ciyar da kwatankwacin haka wannan shekarar.

"Ina ji na a wani yanayi na wadatar zuci, idan na fahimci na saka wani cikin farin ciki," Indianapublicmedia suka yanko maganar Easley.

Malama ta tafka hatsari, ta rasu tana hanyar kai wa dalibanta kyautukan ba-zata

A wani labari na daban, Ghasoon Najimi, wata malamar makarantar kasa da firamare wacce ke kan hanyarta ta zuwa makaranta dauke da kyautuka da niyyar ba wa dalibanta bayan sun lashe jarabawar karshen zangon karatu, ta tafka mummunan hatsarin da ya yi sanadin rasa rayuwarta.

Kara karanta wannan

Sokoto: An kama wadanda suka kashe dalibar da ake zargin ta zagi Annabi

An samu labarin yadda hatsarin ya auku a birnin Saudi na Samata sanadiyyar shiga gabanta da wani abun hawa ya yi. Masu amfani da kafafan sada zumuntar zamani sun yi jimamin mutuwar.

Mutane da dama daga birnin sun halarci jana'izar ta. Gwamnan Jazan, Prince Muhammad bin Nasir bin AbdulAziz, ya bayyana alhininsa bisa mutuwar da jajirtacciyar kuma hazikar malamar.

Kafin mutuwarta, Ghasoon Najimi mahaifiya ce ga 'ya'ya hudu da cikin na biyar. Ta so bawa dalibanta kyautar ba-zatar da ta shirya, jaridar Life In Saudi Arabia ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng