Yau take ranar sallah: Hotunan yadda al'ummar Musulmi suka sallaci Idi a Nijar
- Al'ummar Musulmi a Jumhuriyar Nijar sun yi bikin karamar Sallah a yau Lahadi, 1 ga watan Mayu
- Hakan ya biyo bayan sanar da batun ganin jinjirin watan Shawwal da majalisar koli ta musulunci da gwamnatin jihar ta yi a ranar Asabar
- A hotunan da suka yadu a shafukan sadarwa, an gano mutane a masallacin idi cikin shiga ta alfarma
Nijar - A yau Lahadi, 1 ga watan Mayu ne al’ummar Musulmi suka yi sallar idi a Jamhuriyar Nijar bayan sanar da ganin jinjirin watan Shawwal a kasar, lamarin da ya kawo karshen azumin Ramadana a kasar, sashin Hausa na BBC ta rahoto.
Al’ummar kasar daga bangarori daban-daban sun tabbatar da ganin jinjirin watan na Shawwal a daren ranar Asabar, 30 ga watan Afrilu, inda majalisar koli ta musulunci da gwamnatin kasar suka tabbatar da hakan bayan gudanar da cikakken bincike.
Ba a yi sallah ba a kasashe da dama ciki harda Saudiyya da Najeriya sakamakon rashin ganin wata. Hakan na nufin sai gobe Litinin za a sallaci idi a kasashen.
A hotunan da BBC Hausa ta wallafa, an gano al’ummar musulmi manya da yara a masallacin idi cikin shiga ta alfarma.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ga hotunan a kasa:
Wasu Musulmai a Sokoto sun yi watsi da umarnin Sultan, sun gudanar da Sallah yau Lahadi
A wani labarin, mun ji cewa wasu Musulmai a jihar Sokoto sun gudanar da Sallar Idi yau Lahadi wanda ya saɓa wa umarnin Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, wanda ya ayyana ranar Litinin a matsayin ranar Eid-ul-Fitr.
Daily trust ta rahoto cewa a ranar Asabar, Sarkin Musulmai ya sanar da cewa ba'a ga jinjirin watan Shawwa 1443AH ba a sassan Najeriya.
Mafi yawan Musulman, waɗan da mabiya ne ga Sheikh Musa Lukwa, sun gudanar da Sallar idi wato ƙaramar Sallah da misalin ƙarfe 8:00 na safiyar Lahadi.
Asali: Legit.ng