Jami'an tsaro a kasar Saudi Arabia sun damke mabarata a Masjid Al-Haram
- Jami'an tsaro sun yi ram da mabarata da dama a masallacin Harami, bayan an kamasu dumu-dumu suna bara don samun sullala daga jama'a
- Cikin wadanda aka kama akwai wani 'dan kasar Indiya, wani wanda ya kawo ziyara daga kasar Morocco a wajen masallacin da wani 'dan kasar Yemeni mai amfani da sandar guragu
- Shari'ar da ke yaki da bara ta sanar da cewa ta fara kama mabarata tare da yanke musu hukuncin ko dai daurin shekara daya a gidan yari ko kuma tarar SR100,000
Makkah - Jami'ai a kasar Saudi sun yi ram da mazauna da masu karya dokar da aka kama suna bara a Makkah, wadanda suka hada da cikin dukkan manyan masallatai 2 na Annabi, jaridar The Islamic Inforrmation ta ruwaito.
Kamar yadda hukumomin Saudi suka bayyana, an yi ram da wani mazaunin kasar 'dan kasar Indiya a harabar babban masallacin da wani 'dan kasar Morocco a wajen masallacin bayan an kamasu suna bara don su samu tausayawa daga masu bauta.
Haka zalika, Saudi Gazette ta ruwaito cewa, an hada da wani da ya karya doka 'dan kasar Yemen a jerin sunayen wadanda aka kama, wanda ya yi amfani da sandar guragu ya nuna cewa yana da nakasa don ya roki mutane.
Har ila yau, ya dauka tsawon lokaci yana amfani da karamin 'dansa wajen neman abun duniya ta hanyar gungura shi a kan kujerar guragu don ya maulaci sulalla daga jama'a. Sai dai an gano yadda yaron ke da cikakkiyar lafiya.
Don hani a kan bara, Saudi Arabiya ta saka tsauraran matakai
Kamar yadda shari'ar da ke yaki a kan bara ta bayyana, wacce ta haramta duk wasu nau'ika da fannunka na bara a masarautar, ta fara kama wadanda suka dauki bara a matsayin sana'a.
Kamar yadda jami'an tsaron Saudi Arabiya suka sanar, duk wanda aka kama yana bara ko karfafawa, amincewa ko tallafawa bara cikin kowanne yanayi, za a yanke mishi hukuncin dauri na shekara daya a gidan yari ko a ci shi tara SR100,000.
Hajj 2022: Saudi Arabia ta kayyade shekarun mahajjata, duk wanda ya wuce 65 bashi da rabo bana
A wani labari na daban, a ranar Asabar, Ma'aikatar Hajji da Umara ta Saudi Arabiya ta sanar da makurar shekaru 65 ga mahajjatan da zasu yi aikin Hajjin wannan shekarar. Ma'aikatar ta dakatar da wadanda suka shigar da bukatar yin aikin Hajji da suka kai shekaru 65 kafin watan Afirilu.
Sa dokar Hajjin za ta zama alkhairi ga wadanda basu kai shekaru 65 ba. Hukuncin zai shafi mahajjatan da suka wuce shekaru 65, da kuma wadanda suka shigar da bukatar su da dattawa, mata ko tare da iyayensu a matsayin Muharramansu.
Asali: Legit.ng