An Gano Inda Ɗalibin Da Ya Ɓace Bayan Ya Sanya Kuɗin Makarantarsa A Caca Yake, An Miƙa Shi Hannun Iyayensa
- An gano inda dalibin kasar Uganda, wanda ya bace bat a farkon watan nan bayan tafka asarar KSh 20,000 (N71,781.78), na kudin makarantarsa a caca yake
- ‘Yan sanda sun tsinci Julius Osuta, wanda ya ke aji na farko a Jami’ar Kyambogo, inda suka mika shi ga iyayensa
- Dama iyayensa basu san ya bace ba har sai da ‘yan ajinsu suka kira mahaifinsa inda suka tambayeshi inda dansa yake
Uganda - An gano inda Julius Osuta, wani dalibi na ajin farko a Jami’ar Kyambogo da ke kasar Uganda yake bayan ya bace a ranar 7 ga watan Afirilu bayan ya yi asarar kudin makarantarsa, kuma an mika shi a hannun iyayensa.
Wannan ne karo na biyu da aka ji labarin Osuta tun bayan batarsa ta farko wanda aka ganshi a ranar 9 ga watan Afirilu kafin ya kara boyewa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Bayan gano shi, an mika shi a hannun iyayensa kamar yadda Daily Monitor ta ruwaito.
An samu bayani akan cewa an ga Osuta a tashar Arua da ke Kampala kuma an mika shi a hannun iyayensa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan yankin Kampala, Luke Owoyesigire ya sanar da manema labarai cewa ya yi asarar fiye da KSh 20,000 (N71,781.78) wurin caca.
Osuta ya amshi kudin ne a hannun mahaifinsa wanda ya ba shi musamman don biyan kudin makarantarsa.
Tsokacin jama’a karkashin wallafar
Tibaringanira ya ce:
“Muna da yawa wadanda suka lamushe kudin makarantarsu amma yanzu muna da muhimmanci ga iyayenmu. Akwai bukatar a zaunar da shi don tattaunawa muna fatan zai gyaru.”
Tuti Tuti ya ce:
“Ya bar karatun kawai ya fara dako a tashar Arua. Bayan karatu, babu ayyukan yi.”
Maggie Nampijja ya ce:
“Na yi farin ciki da iyayensa har yanzu da ransu. Iyayen su tattauna da shi a natse don ya mayar da hankali akan karatu.”
Musa Lemeri ya ce:
“Ya yi tunanin zai samu riba ne daga kudin makarantar sai ga shi ya shiga matsala. Su yafe mishi kawai.”
Katsinsa: Ɗan Shekara 22 Ya Sace Wa Dattijuwa Kuɗinta Na Garatuti Baki Daya, Ya Siya Mota Da Babur
A wani labarin, Yan sanda a Jihar Katsina, a ranar Litinin sun yi holen wani Aliyu Abdullahi mai shekaru 22, mazaunin Kasuwar Mata Street a Karamar Hukumar Funtua saboda damfarar wata tsohuwa.
Ya wawushe mata dukkan kudinta na garatuti ta hanyar amfani da katin ta na banki wato ATM inda ya siya mota da babur da kudin, Vanguard ta ruwaito.
An taba kama mayaudarin, wanda ya kware wurin damfarar mutane ta hanyar sauya musu katinsu na ATM a baya amma daga bisani ya fito daga gidan yari kuma ya cigaba da laifin, rahoton Vanguard.
Asali: Legit.ng