Google ta aika muhimmin sako ga Mawallafa game da yaƙin Rasha da Ukraine

Google ta aika muhimmin sako ga Mawallafa game da yaƙin Rasha da Ukraine

  • Google ta aika da saƙo ga mawallafa labarai dake ɗakko rahoton yaƙin dake gudana tsakanin Rasha da Ukaraniya
  • Kamafanin ya bayyana cewa ba zata biya ko sisi ba a tsarin Adsense ɗinta ga duk wanda ya zuzuta, amfani ko kuma watsa yaƙin
  • Haka nan Google ta shiga layin sauran Kamfanonin da suka ƙauracewa kasuwannin Rasha don nuna goyon baya ga Ukraine

Kamfanin bincike Google ya tura kakkausan sakon gargaɗi ga mawallafanta, waɗan da ke kokarin cin riba da yaƙin dake gudana tsakanin Rasha da Ukraine.

Kamfanin ya ce zai dakatar da tsarin biya ga duk wani labari da ya maida hankali wajen watsawa, zuzutawa ko ya nuna amincewa da yaƙin.

Google ta ɗau mataki game da yaƙin Ukraine da Rasha.
Google ta aika muhimmin sako ga Mawallafa game da yaƙin Rasha da Ukraine
Asali: Getty Images

Google ta fara zartar da matakin

A wani sakon Email da Google ta tura wa ma'aikatanta wanda Legit.ng Hausa ta gani, Kamfamin ya ce tuni ya fara dakatar da irin waɗan nan abubuwa da suka shafi yaƙin Ukarine, tun bayan fara mamayar Rasha a ƙasar a ranar 24 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

2023: Atiku ya ɗaukar wa Yan Najeriya alkawari biyu idan ya zama shugaban ƙasa

Bugu da ƙari Kamfanin ya ce ba zai bar duk wani labari da ya ɗora laifin kan mutanen da ake zalunta ba ko kuma ya yi ikirarin cewa Ukraine ta aikata laifukan yaƙi.

Katafaren Kamfanin Fasahan ya nuna damuwa matuka game da yawan labaran ƙarya dake ƙara yaɗuwa, inda ya ce ba zai lamurci cigaba da zuzuta rikicin ba.

A cewar sakon, Google ta yi haka ne domin nuna matsayarta da kuma karin haske kan dokokinta na wallafa domin kiyayewa.

Google ta ce:

"Saboda yaƙin dake wakana a Ukraine, zamu dakatar da biyan duk wani labari da ya zuzuta ko ya nuna amincewa da yaƙin. Kusani cewa mun riga mun fara zartar da haka kan labaran da suka shafi yaƙin a Ukraine idan ya saɓa wa tsarukan mu."

Kara karanta wannan

Ana Wata Ga Wata: Babbar Kotu Ta Tsige Shugaban Jam'iyyar PDP Kan Kuskure Ɗaya

"Mun tura wannan sakon ne domin bayani da karin haske, a wata manhagar kuma, dokar kiyaye wa ga mawallafan mu game da abin da ya shafi wannan rikicin."
"Matakin dakatarwan ya hau kan, amma ba iyakar su kenan ba, ikirarin cewa mutanen da ake zalinta su suka jawo wa kan su bala'i, ko abunda da ya shafi haka, kamar labarin Ukraine ta saɓa dokar yaƙi ko kuma ita ke farmakan mutanenta."

A wani labarin kuma Tunatarwa: Abubuwan da ya kamata kusani masu muhimmanci game da watan Azumin Ramadan

Azumtar watan Ramadana na ɗaya daga cikin abubuwa 5 da aka gina Musulunci a kan su kuma shi ne wata na Tara.

Kowane Musulmi an umarce shi ya Azumci watan na kwana 29 ko 30, amma akwai wasu rukunin mutane da Allah ya musu rangwame.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262