Sunayen biloniyoyi 87 na duniya: Dangote ya fi kowa kudi a Afrika, Elon Musk ya ninka shi sau 15

Sunayen biloniyoyi 87 na duniya: Dangote ya fi kowa kudi a Afrika, Elon Musk ya ninka shi sau 15

  • Jerin sunayen wadanda suka fi kowa kudi a duniya da Forbes ta saki na shekarar 2022 ya fita, inda 'yan kasar Amurka suka mamaye kusan goma na farko
  • Kamar yadda mujallar abar girmamawa ta bayyana, a halin yanzu duniya na da biloniyoyi 2,668, 87 kasa da na 2020
  • Kamar yadda Forbes ta bayyana, Elon Musk wanda yazo na farko, dukiyarsa ta ninka ta Aliko Dangote, mutumin da ya fi kowa kudi a Afirka, sau 15

Mujallar Forbes ta saki jerin sunayen wadanda suka fi kowa dukiya a duniya, wanda takwas daga cikin goma na farko 'yan kasar Amurka ne, sai daya daga Faransa da kuma daya daga Indiya.

Har yanzu, Amurka ce ke mulkar duniya, wacce ke da biloniyoyi 735 da jimillar dukiyar $4.7 tiriliyan, duk da Elon Musk, wanda yazo na farko a jerin sunayen biloniyoyin duniya a karo na farko sama da Jeff Bezos.

Kara karanta wannan

NDLEA ta kama sinkin hodar iblis 101 a cikin bargunan yara a Legas

Sunayen biloniyoyi 87 na duniya: Dangote ya fi kowa kudi a Afrika, Elon Musk ya ninka shi sau 15
Sunayen biloniyoyi 87 na duniya: Dangote ya fi kowa kudi a Afrika, Elon Musk ya ninka shi sau 15. Hoto daga forbes.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Independent UK ta ruwaito yadda Musk ke da $2 biliyan kacal a shekarar 2012, hakan na nufin ya tara sama da $218 biliyan (sama da N90.62 tiriliyan) cikin shekaru goma.

Jerin sunayen wannan shekarar shine na 36 da Forbes ta saki, kuma ya kunsa sama da biloniyoyi 1,000, wandanda arzikinsu ya tumbatsa fiye da shekarar da ta gabata.

Haka zalika, Forbes ta ambaci sunan Aliko Dangote a matsayin wanda ya fi kowa kudi a Afirka, duk da ya gaza shiga sunayen manyan masu kudin duniya guda 100 a jerin sunayen 2022.

Dangote mutum na 130 a cikin jerin sunayen da $14 biliyan a matsayin jimillar dukiyarsa. Wanda ya biyo bayan hamshakin 'dan kasuwan Najeriyan a Afirka shine 'dan Afirka ta Kudu, Johon Ruppert da danginsa. Wanda sunansa ya zo na 230 a jerin sunayen da $8.9 biliyan a matsayin jimillar dukiyarsa.

Kara karanta wannan

Duniya juyi: Attajiran Najeriya na kara kudancewa yayin da sauran na duniya ke ganin ragi

Wani 'dan kasar Afirika ta Kudu, Nicky Oppenheimer ya zo na uku a Afirka, sannan na 241 a fadin duniya tare da $8.7 biliyan a matsayin jimillar dukiyarsa.

Dan kasar Misira dan kwangila da zuba hannun jari ya zo a na 304 da jimillar dukiyarsa $7.7 biliyan.

Mike Adenuga na Najeriya ya shiga jerin sunayen wadanda suka fi kowa kudi a Afirka guda 5 a matsayin na 324 a duniya da $7.3 biliyan a matsayin jimillar dukiyarsa.

Sai dai a baya Legit.ng ta ruwaito yadda Elon Musk, daya daga cikin mamallakan Tesla, ya mayar da kudin da ya kashe wajen zama wanda yafi kowa kaso a Twitter, bayan ya samu ribar N6.36 tiriliyan a rana.

Sunaye: Jerin kasashen duniya 5 masu tarin biloniyoyin duniya

A wani labari na daban, kamar yadda jerin biloniyoyi na duniya da Forbes ta fitar karo na 36 ya nuna, akwai biloniyoyi 2,668 masu arzikin $12.7 tiriliyan a duniya. Duk da yaki, annoba da kuma tashin kadarori a kasuwanni, hakan bai girgiza wadannan mashahuran masu arzikin na duniya ba.

Kara karanta wannan

Sunaye: Jerin kasashen duniya 5 masu tarin biloniyoyin duniya

An gano biloniyoyi 2,668 a fadin duniya a 2022 kasa da 2,755 da aka samu a 2021 masu dukiya wacce ta kai darajar $12.7tirliyan kasa da $13.1 tiriliyan.

Kasashen duniya biyar ne suka samar da yawancin biloniyoyin duniya. Babu wanda ya wuce Elon Musk a arziki, wanda shi ne yanzu ya fi kowa kudi a duniya kuma wannan ne karon farko da ya fara kaiwa wannan matsayin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng