Ramadan 2022: Sunayen limaman da za su jagoranci Tarawih da Tahajjud a Masjid Al Haram
- Hukumomin kasar Saudi Arabia sun saki sunayen limaman da za su jagoranci sallolin Tarawihi da Tahajjud a masallacin Harami dake Makkah na watan Ramadanan shekarar nan
- Sai dai, Haramain sun saki bayani game da raba jagorancin salloli ko lokutan da limaman zasu jagoranci sallar Tarawihi a watan nan mai alfarma
- A yanzu, babu bukatar jamaa da za su yi sallar Tarawihi a masallacin Annabi da su bi dokar dakile korona, sai dai zasu gabatar da alamar tabbatar da suna da cikakkiyar lafiya a manhajar Tawakkalna
Hukumomin kasar Saudiyya sun saki sunayen limaman da za su jagoranci sallolin Tarawihi da Tahajjud a masallacin Harami dake Makkah na watan Ramadanan wannan shekarar. Sakin jerin sunayen limaman yazo ne ta shafin
a ranar 23 ga watan Maris.
Jerin sunayen limaman da zasu jagoranci sallar Tarawihi da Tahajjud a masallacin Harami sun hada da.
Ga sunayen limamai shida da za su jagoranci sallolin Tarawihi da Tahajjud a masallacin Harami cikin watan Ramadanan 2022, wanda za a fara a farkon watan Afrilu.
- Sheikh Abdullah Awad Al Juhany
- Sheikh Abdur Rahman Al Sudais
- Sheikh Saud Al Shuraim
- Sheikh Maher Al Muaiqly
- Sheikh Yasir Al Dawsary
- Sheikh Bandar Baleelah.
Duba da sunayen limaman da aka saki, za'a iya cewa babu bakon limamin da aka naɗa a wannan shekarar.
Sai dai, shafin Haramain sharifain ya saki bayani game da raba jagorancin salloli ko lokutan da limaman za su jagoranci sallar Tarawihi a watan Ramadanan, kamar haka.
Dama, Musulmai a faɗin duniya sun dade suna matsanancin farin cikin samun labari mai dadi game da yadda za a gudanar da sallolin Tarawihi a masallacin Harami da masallacin Annabi a watan Ramadanan wannan shekarar a cike.
Shugabannin lamurran masallatan guda biyu sun sanarwa ƴan gari da baƙi daga ƙasashen duniya yadda za a bar su suyi sallar Tarawihi a masallatan guda biyu.
Musulman fadin duniya sun ji daɗin jin wannan labarin duba da yadda mutane da dama basu samu damar yin sallar Tarawihi na shekarar 2021 a masallacin Harami ba, wanda mutane ƙalilan aka bawa damar yin sallar, wadanda suka haɗa da shuwagabannin masallacin Haramin tare da mazauna kasar, saboda a lokacin ne gwamnati ta tilasta kulle gami da haramtawa baƙi daga wasu kasashen shiga masallacin domin gudun yaɗuwar cutar Korona.
A halin yanzu, ba a bukatar masu bautan da zasu halarci sallar Tarawihi a masallacin Annabi da su bi dokar korona.
Kawai ana bukatar su gabatar da alamar da zai tabbatar da suna da cikakkiyar lafiya a manhajar Tawakkalna kafin su shiga masallatan guda biyu.
Asali: Legit.ng