Matar Da Ta Fi Kowa Tsayi a Duniya Tace Ta Dade Tana Neman Saurayin Da Ya Dace Da Ita Amma Abin Ya Faskara
- Wata mata ‘yar kasar Rasha mai tsayin sawu 6 da inci 9 ta bayyana irin gwagwarmayar da take yi wurin neman saurayin da ya dace da ita
- Kasancewar ta kafa babban tarihi a Guinness World Record a matsayin wacce ta fi kowa dogayen kafafu, tana fuskantar kalubale wurin samun saurayi
- A cewarta duk samarin da ke tunkarar ta sun yi mata gajarta, sannan dogayen da take haduwa da su ba sa son soyayya da ita saboda tsayin ta ya yi musu yawa
Rasha - Wata mata mai tallace-tallace ‘yar kasar Rasha mai tsayin sawu 6 da inci 9 ta bayyana damuwar ta akan kalubalen da take fuskanta wurin samun saurayin da ya dace da ita, LIB ta ruwaito.
Ekaterina Lisina wacce ta kafa tarihin zama mace mafi tsayi a duniya ta shiga Guinness World Record a matsayin “wacce ta fi kowa tsawon kafafu a duniya”, hakan yasa ta fi maza da dama tsayi kuma take wahala wurin samun saurayin da ya dace da ita.
‘Yar wasan kwallon kwando ce a baya, daga bisani ta koma harkar tallace-tallacen sutturu.
Tsayin mahaifin Ekaterina ya kai sawu 6 da inci 6, yayin da mahaifiyarta ta kai sawu 6 da inci biyu, kuma ta ji tsoro yayin da ta gane cewa zata iya kamo iyayenta tsayi.
Ta bayyana irin mijin da take so
Kamar yadda ta ce:
“Kun san irin matsalar, idan ka hadu da saurayin da kafi tsayi sosai ko kuma ka hadu da dogo wanda ya yi maka amma kuma ba ka yi mishi ba saboda ka cika tsayi.”
Ta razana ne bayan ta zarce iyayen ta tsayi. Kamar yadda ta shaida, tana wahala wurin samun namiji mai tsayi wanda ya dace da ita, LIB ta ruwaio.
A cewarta, ba za ta iya tarayya da namijin da tsayin sa ya gaza sawu 5 da inci 7 ba.
Yayin da aka tambaye ta idan ta taba soyayya da wanda ya yi kasa da sawu 5 da inci 7, cewa ta yi bata taba ba saboda ya yi mata gajarta.
Kamar yadda ta ce:
“Bambancin ya kai sawu daya, kuma mata da dama ba sa soyayya da wanda suka fi tsayi ko da kuwa kadan ne ballantana har ya kai sawu daya.”
Asali: Legit.ng