Rasha Za Ta Kai Wa Wasu Ƙasashe Hari, Zelensky Ya Gargaɗi Shugabannin Kasashen Duniya
- Volodymyr Zelensky, Shugaban Kasar Ukraine ya gargadi sauran kasashen Turai da Yamma cewa Rasha za ta iya afka musu da yaki
- Zelensky ya yi wannan gargadin ne yayin wata hira da aka yi da shi a ranar Litinin inda ya ke rokon NATO da Amurka ta kawo masa dauki
- Shugaba Zelensky ya bukaci NATO da Amurka su haramtawa Rasha ikon ratsa sararin samaniyar Ukraine amma kawo yanzu ba su yi hakan ba
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya gargadi kasahen Yamma cewa yakin ba zai tsaya a Ukraine kadai ba - kuma harin da aka kai wa kasarsa zai shafi sauran kasashen duniya.
Yayin hira da aka yi da shi a ABC World News Tonight tare da David Muir a ranar Litinin, Zelensky ya sake jaddada bukatar da ke akwai na tsare sararin samaniyar Ukraine - abin da ya bukaci NATO da Amurka su taimaka su yi amma hakan bai yiwu ba.
"Ba zai yiwu mu kyalle Rasha ita kadai ta rika shawagi ba, domin suna mana ruwan bama-bamai, suna harbin min da jiragen yaki da jirage masu saukan ungulu - abubuwa da dama," Zelensky ya ce. "Ba mu ke da iko da sararin samaniyar mu ba."
Ya kara da cewa ya yi imanin akwai abubuwan da Shugaban Amurka Joe Biden "zai iya yi" don kawo karshen yakin kuma na yi imani da hakan. Zai iya yin hakan," In ji Zelensky.
Matakin Amurka da NATO
Amurka da NATO sun ki amincewa da haramtawa Rasha ratsa sararin samaniyar Ukraine, suna gargadin cewa hakan na iya bawa Rasha damar kaddamar da cikakken yaki da kasashen Turai.
A ranar Litinin, Amurka ta ce har yanzu Biden yana kan bakansa na kin tsinduma sojojin Amurka cikin rikicin.
Yakin nan yana iya shafar sauran kasashen duniya, Zelensky
"Kowa na tunanin mu na da nisa daga Amurka ko Canada. A'a, muna wannan matsayin na yanci ne tare. Idan kuma an take mana hakki ko yanci, ya kamata ku kare mu. Domin mu ne na farko. Amma abin zai zo kanku. Domin wannan dodon ba zai dakata ba bayan ya cinye mu, zai cigaba da neman kari ne." in ji Zelensky.
Saurari karin bayani ...
Asali: Legit.ng