Ukraine: Ƙasashen Yamma Sun Yi Abubuwa Tamkar Ƴan Fashin Daji, In Ji Rasha
- Gwamnatin kasar Rasha ta soki Amurka da sauran kasashen yamma inda ta kwatanta abin da suke yi da 'yan fashin daji
- Dimitry Peskov, mai magana da yawun Kremlin ne ya furta hakan yayin da ya ke magana kan takunkumin da kasashen Yamma ke saka wa Rasha sakamakon harin da ta kai wa Ukraine
- Peskov ya ce idan aka saka takunkumi kan makamashin da Rasha ke sayarwa kasashen duniya tabbas farashin makamashi zai yi tashin gauron zabi
Fadar gwamnatin Rasha, a ranar Asabar ta ce kasashen Yamma suna nuna halaye tamkar yan bindiga amma Rasha ta yi girman da ba za a iya ware ta daga duniya ba domin duniya ya fi Amurka da Turai girma.
Mai magana da yawun Kremlin, Dmitry Peskov, ya shaida wa manema labarai cewa kasashen Yamma sun fara yi wa Rasha 'fashin daji na tattalin arziki' amma Moscow za ta yi martani, rahoton Daily Trust.
Bai yi karin bayani game da irin matakin da za su dauka ba amma ya ce mataki ne da zai amfani Rasha.
"Hakan ba ya nufin an ware Rasha a gefe guda," Peskov ya shaida wa manema labarai.
"Duniya ya yi wa Amurka da Turai girma ta yadda za su iya ware wata kasa, balantana kasa mai girma kamar Rasha. Akwai wasu kasashe masu girma a duniya."
Saka wa Rasha takunkumi kan makamashi zai janyo tashin farashi, Peskov
Peskov ya ce idan Amurka ta saka takunkumi a kan makamashi da Rasha ke sayarwa kasashen duniya, hakan zai janyo tashin gauron zabi a farashin makamashi a kasuwan duniya, rahoton Reuters.
Kakakin na Kremlin ya ce har yanzu akwai hanyoyin tattaunawa tsakanin Moscow da Washington.
Russia vs Ukraine: Taliban Ta Faɗa Wa Rasha Ta Yi Sulhu da Ukraine
A wani rahoton, Taliban ta yi kira ga Rasha da Ukraine sun warware rikicin da ke tsakaninsu ta hanyar lumana watanni bayan ta halaka mutanen da ba su ji ba ba su gani ba bayan karbar mulki a Afghanistan.
A cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin Twitter na Taliban, mai suna Islamic Emirate of Afghanistan, kungiyar mayakan ta ce tana damuwa bisa yiwuwar asarar rayukan farar hula.
A karkashin wani hatimin hukumar harkokin kasashen waje na kasar - wanda ya yi kama da irin wanda Amurka ke amfani da shi - Taliban ta yi kira da cewa a yi zaman tattaunawa tsakanin Rasha da Ukraine kuma a tsare lafiyar yan Afghanistan da ke Ukraine.
Asali: Legit.ng