Kotun Musulunci ta yanke wa wata mata hukuncin kisa kan sakonni a dandalin Whatsapp
- Wata kotu ta yanke wa matashiya yar shekara 26 hukuncin kisa bisa aikata batanci ga Annabi Muhammad (SAW) ta Whatsapp
- Rahoto ya bayyana cewa matar ta na amfani da Whatsapp da kuma Facebook wajen yin kalamai da sanya wasu abubuwa na batanci
- Baya ga hukuncin kisa, kotun ta kuma ci tarar matashiyar, kuma ta yanke mata zaman gidan kaso na shekara 20
Kotun ƙasar Pakistan, ta yanke wa wata mata yar shekara 26, Aneeqa Atteeq, hukuncin kisa bisa zargin tura sakonnin ɓatanci a WhatsApp da Facebook.
The Nation ta rahoto cewa kotun ta kama ta da aikata batanci ga Annabi Muhammad, (S.A.W) a wasu sakonni da ta tura.
Rahotanni sun bayyana cewa ta gamu da mutumin da ya maka ta a kotu ne a wata manhajar wasanni, kuma suka cigaba da gaisawa a dandalin Whatsapp.
An yanke mata hukuncin ne a Rawalpindi, ranar Laraba, biyo bayan shigar da ƙararta kan saba wa dokokin yanar gizo da batanci ga Annabi na ƙasar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yadda ta aikata laifin
The Guardian ta rahoto cewa, matar ta gamu da mutumin da ya fallasa asirin ta, wanda shi ma ɗan ƙasar Pakistan ne, a dandalin sada zumunta.
Mutanen biyu sun fara gamuwa da juna ne a wata manhajar wasanni, daga bisani kuma suka cigaba da fira a dandalin WhatsApp.
Mutumin ya bayyana cewa ta tura masa sakonni bila adadin na batanci ga Annabin tsira, kuma tana amfani da WhatsApp wajen tsokaci a kan abin da ya shafi imani.
Kazalika ya ce matar tana kuma amfani da shafinta na dandalin Facebook, wajen sanya wasu abubuwa da suke alaƙa da batanci ga Annabi.
Takardar ƙarar kotun tace:
"Da gangan kuma tana sani, matar tana kazantar da mutane masu tsarki. kuma tana cin mutuncin mabiya addinin musulunci."
Shin matar ta amsa laifinta?
Wacce ake zargi, Ateeq, mai bin tafarkin Musulunci, ta musanta zargin da ake mata, inda ta kara da cewa mutumin ya ja ta da firar Addini ne domin ya samu shaidar da zai ɗau fansar ƙin amince masa da ta yi.
Lauyan dake kare matar, Syeda Rashida Zainab, tace ba zai yuwu ta yi martani kan hukuncin kotu ba, "domin lamarin yana da matukar haɗari."
Bayan hukuncin kisa, kotu ta kuma ci tarar matar tare da hukuncin shafe shekaru 20 a gidan gyaran hali.
Rahoto ya nuna cewa hukuncin kisan da aka yanke mata na bukatar tabbatar wa daga babbar kotu dake Lahore, kuma tana da damar ɗaukaka ƙara.
A wani labarin na daban kuma Wata mata ta shigar da mjinta ƙara kotu, ta nemi a raba su saboda yana cizon ta kuma yana lakada mata dukan tsiya
Wata mata ta maka maigidanta a gaban kotu, ta nemi alkali ya datse igiyoyi uku na aurensa dake kanta nan take.
Matar ta shaida wa kotu cewa mijinta yana zaluntar ta, ga cizo wani lokacin ya lakaɗa mata dukan tsiya idan ba ta yi abinci ba.
Asali: Legit.ng