Ina fatan ninka yawan 'ya'ya na, Magidanci mai yara 9 da ke cikin tsananin talauci da rashi
- Magidanci dan kasar Zimbabwe mai suna Ernest Chinuwo da ke rayuwa a daki daya tare da 'ya'yansa 9 ya ce yana fatan samun ninkin 'ya'yansa
- Sun rayuwars a wani ragargazajjen kwari da ke wajen garin inda kowacce rana yaran ke fita su nemo abinci tare da siyar da gawayi da itace
- A cewar magidancin, ya yarda cewa haifar yara masu yawa ne hanya mai sauki ta samun arziki, don haka yana son cigaba da hayayyafa duk da fatarar da ya ke ciki
Zimbabwe - Wani magidanci dan asalin kasar Zimbabwe ma 'ya'ya 9 wanda ke zaune a daki ciki da falo, cike da abin mamaki ya bayyana burinsa na ninka yawan yaran da ya mallaka.
Ernest Chinuwo, ya na zaune tare da iyalinsa a wani ragargajajjen bukka kuma a wani kwari mai ruma a wajen garin Usanga a Chipinge, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.
Mutane sun zub da hawaye bayan ganin bidiyon babban sarki a Najeriya yana waƙa tare da iyalansa dab da zai rasu
Kafar watsa labaran kasa ZBC ta ruwaito yadda mutumin ya ce ya na zama a kwarin, bayan wani ya sa shi ya zama mai kula da gurin. Mai gurin ya na zaune a kasar Afirika ta kudu.
Mahaifin yara 9 wanda ke zaune a daki daya tare da iyalin sa ya ce ya na burin ninka yawan yaran da ya mallaka.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Bayan amincewa da yadda iyalin sa su ke rayuwa da kyar, Chinumo ya bayyana yadda yaran sa su kan tashi da wuri su yi fadi tashi dan neman abinda za su ci a cikin garin Chipinge duk da ya na da kuruciya. Ya ce yaran sa suna yin itace wanda suke sayarwa tare da gawayi da 'ya'yan itace kamar ayaba.
Duk da tsananin rayuwar da suke ciki, mutumin ya na da burin mallakar wasu yaran kamar yadda ya yi imani Allah ne zai taimake sa. Marigayiyar matar sa ta haifi yara 9, wadanda suka hada da 'yan biyu sau 4. Ya yarda kamar wani sashi na al'umma, yara su ne mafi arhar hanya neman na kai.
Kano: Yadda rikicin sarauta ya mamaye kauyen Langel da ke Tofa
A wani labari na daban, rikici ya kacame a kauyen Langel da ke karamar hukumar Tofa ta jihar Kano kan wanda zai zama dagacin garin. An tattaro cewa, rikicin da ya fara kwanaki kadan da suka gabata ya yi sanadin arangama tsakanin mazauna yankin wanda hakan ya bar wasu da miyagun raunika, Daily Trust ta ruwaito.
Tsohon dagacin ya bukaci babban dan sa, Alhaji Abubakar Langel, da ya karba ragamar sarautar amma wasu mazauna yanki sun yi na'am da wannan hukuncin.
Kamar yadda magoya bayan Alhaji Abubakar suka sanar, ya na aiki tukuru tun kafin mahaifinsa ya yi murabus kuma mazauna yankin sun yanke hukuncin goyon bayansa wurin gadon mahaifinsa.
Asali: Legit.ng