An sake nada ‘Yar Najeriya, Amina Mohammed a kujerar Majalisar dinkin Duniya a karo na 2

An sake nada ‘Yar Najeriya, Amina Mohammed a kujerar Majalisar dinkin Duniya a karo na 2

  • António Guterres ya zabi Amina J. Mohammed ta zarce a kujerar sakatariyar mataimakiyar UN
  • Da take magana a shafinta na Twitter, Miss Amina J. Mohammed ta tabbatar da cewa ta karbi mukamin
  • Amina J. Mohammed ‘Yar asalin Najeriya ce da take rike da kujerar mataimakin shugaban majalisar UN

United States - Shugaban majalisar dinkin Duniya, Mr. António Guterres ya bada sanarwar sake nada Ms. Amina J. Mohammed a matsayin mataimakiyarsa.

A wata sanarwa da ta fito daga majalisar dinkin Duniya, an ji cewa António Guterres ya zabi Amina J. Mohammed ta cigaba da rike kujerar da ta ke a kai.

Guterres ya yabi Mohammed, yace ta kawo sauye-sauyen da ba a taba gani ba a tarihin majalisar.

Daga cikin kokarin da tsohuwar Ministar Najeriyar tayi akwai tabbatar da cewa kasashen da ke karkashin UN sun dabbaka manufofin SDG da aka shigo da su.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Diyar sarki ta rasu kwanaki kadan bayan rasuwar mahaifinta

A shekaru biyar da suka wuce, an ga yadda kasashen Duniya suka rungumi kadarorin SDG da nufin kawo cigaba a fadin Duniya da inganta rayuwar mutane.

An sake nada ‘Yar Najeriya, Amina Mohammed a kujerar Majalisar dinkin Duniya a karo na 2
Amina J. Mohammed Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Amina Mohammed ta taka rawar gani wajen yakar matsalolin sauyin-yanayi, sannan kuma ta bada gudumuwa wajen tsare yarjejeniyar nan ta Paris Agreement.

Jaridar nan ta Premium Times ta ce António Guterres ya jinjinawa mataimakiyar ta sa a kan kokarin da tayi wajen rage radadin tasirin annobar cutar COVID-19.

Na ji, na karba - Amina Mohammed

Da take bayani a shafinta na Twitter, Ms Mohammed ta karbi wannan mukami da aka sake ba ta.

“Ina mai kankan da kai da karbar wa’adi na biyu a matsayin mataimakiyar sakatariyar UN tare da @antonioguterres.”
“Zan fara wannan aiki da alfaharin zama mace ‘Yar Najeriya da nufin cika alkawuran SDG. Za mu tafi tare da kowa.”

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mummunar gobara ta yi kaca-kaca da wani gida, uwa da jaririnta sun kone a Kano

- @AminaJMohammed

Daga ina Mohammed ta zo UN?

Rahoton ya ce idan za a tuna Amina Mohammed ta rike Minista a gwamnatin Muhammadu Buhari kafin ta zama mataimakiyar sakatariyar majalisar UN a 2017.

Mutumiyar Najeriyar tayi aiki da tsohon shugaban majalisar dinkin Duniya, Ban Ki-moon a matsayin hadimarsa bayan tayi aikace-aikace da gwamnatin Najeriya.

Najeriya tayi rashi

Rahotanni sun ce tsohon shugaban kasa a Najeriya, Cif Ernest Shonekan ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayi Ernest Shonekan ya rike mulki na ‘yan kwanaki kadan a Najeriya. Cif Shonekan bai dade a kan mulki ba sai Janar Sani Abacha ya yi masa juyin-mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel