Ba a gama fahimtar Omicron ba, sabon nau’in kwayar cutar COVID-19 ya sake bayyana

Ba a gama fahimtar Omicron ba, sabon nau’in kwayar cutar COVID-19 ya sake bayyana

  • Masana kiwon lafiya sun gano wani nau’in cutar COVID-19 wanda zai iya yi wa magani taurin kai
  • An fara samun bullar cutar ne a yankin Marseille, Faransa, da wahala idan cutar ta bar kasar Turan
  • A cibiyar The Méditerranée Infection University Hospital Institute aka gano wannan samfuri kwanaki

France - Masana kimiyya da malaman lafiya sun samu labarin bullar wani samfuri na kwayar cutar COVID-19 a Faransa, AU News ta fitar da wannan rahoto.

Wannan sabon nau’i da kwayar cutar COVID-19 da aka sa wa suna da “variant IHU” ko kuma B. 1.640.2 ya bayyana ne a kasar Faransa a a watan da ya wuce.

Rahoton da muka samu a ranar Litinin yace akalla mutane 12 aka samu sun kamu da cutar a yankin Marseilles a kasar Faransa, kuma cutar ta kwantar da su.

Kara karanta wannan

Dawo-dawo: Tsohon Shugaban kasa Jonathan ya yi zaman sirri da masu so ya koma kan mulki

Masanan da ke aiki a cibiyar lafiya ta The Méditerranée Infection University Hospital Institute (IHU), suka fara bincike a kan wannan cuta da ta shigo gari.

Har zuwa yanzu, hukumar lafiya ta Duniya watau WHO ba ta kammala na ta binciken ba tukuna.

Cutar COVID
COVID-19 IHU ya bullo Hoto: www.reuters.com
Asali: UGC

IHU ya saba da magunguna

Ana zargin an haifi samfurin cutar ne a sakamakon shiga Kamaru a yammacin Afrika a shekarar 2021. Cutar ta kara gagarar masana domin ta saba da magani.

Sai dai abin farin cikin shi ne, masana na ganin wannan samfuri ba ya yawo kamar takwarorinsa.

Haka zalika ba a tunanin har yanzu kwayar cutar IHU ta fita daga iyakokin kasar Faransa, ko da ana zargin ta shiga jikin mutane a kasar Birtaniya kwanan nan.

Kara karanta wannan

Dan kasuwa ya daba wa matarsa wuka har lahira bayan ya dirka mata saki a Adamawa

Philippe Colson ya rubuta takarda

Farfesa Philippe Colson wanda shi ne shugaban sashen da ya gano samfurin cutar, ya fitar da takarda kan abubuwan da ya gano a binciken da ya yi a Marseille.

Takardar Farfesa Philippe Colson ta nuna cewa wanda ya fara kamuwa da cutar wani mutumi ne da aka yi wa rigakafin COVID-19 da ya ziyarci kasar Kamaru a bara.

Bayan wannan mutum ya fara samun matsalar numfashi, sai aka yi masa gwaji a watan Nuwamban 2021 inda aka tabbatar cewa ya kamu da cutar murar.

Magungunan cikin gida

A 2021 ne aka ji cewa Gwamatin tarayya ta hannun majalisar kolin tattalin arzikin Najeriya watau NEC, ta bada dama a kirkiro magungunan COVID-19 na gida.

Gwamnatin Muhammadu Buhari za ta hada kai da masanan ketare domin samun magungunan da za su taimaka wajen yakar kwayar cutar Coronavirus a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel