Wata sabuwa: Wanda yace shi ya kirkiro Bitcoin ya gagara cire kudi a asusu a kasuwar Crypto
- Craig Wright masanin kimiyyar kwamfuta ne wanda ya yi ikirarin shine ya kirkiro Bitcoin. Kwanan nan ya ci nasara a shari'ar da har yanzu al'ummar Bitcoin ke cece-kuce akai
- Bayan da wata kotu a Amurka ta yanke masa hukunci, ya bayyana cewa mutane za su yi imani cewa shi ne ya kirkiro Bitcoin yanzu kam
- Duk da haka, al'ummar Bitcoin suna kalubalantarsa da ya janye ko ya aika kudin da suka kai dala miliyan 1.1 na Bitcoin da ya ce yana sarrafawa
Craig Wright, wanda ya ayyana kansa a matsayin wanda ya kirkiri Bitcoin, yana shirin kaura zuwa wani kauye bayan ya ci nasara a kotu inda ya ce an ayyana shi a matsayin wanda ya kirkiro bitcoin.
Duk da yanke hukuncin, al'ummar Bitcoin ba su gamsu ba kuma sun kalubalance shi da ya aika wani kaso na Bitcoin miliyan 1.1 da ya ce yana da ikon akai zuwa wani asusu don nuna ikon mallakarsa.
Indiatimes ta ce al'ummar Bitcoin ba su amince da Wright ba, kuma mutane da yawa sun nemi kawai ya motsa wani dan karamin kaso na Bitcoin kamar miliyan 1.1 zuwa wani asusu na daban don tabbatar da mallakar tsabar, lamarin da ya faskara ya zuwa yanzu.
Tushen batun a tun farko
A baya Legit.ng ta rahoto cewa matashi abokin kasuwancin Craig Wright ne ya kai kara gaban wata kotu a Amurka kan wani kaso na Bitcoin miliyan 1.1 a hannun Wright, hukuncin da Wright yayi nasara. Yanzu dai matashin ya mutu.
A shekarar 2016, ya fara buga rubutu a wani shafin yanar gizo yana ayyana kansa da cewa shi ne Satoshi Nakamoto sunan da ake alanta wa wanda ya kirkiri Bitcoin.
A cikin sakon, ya kuma ci fariyar tabbatar da hakan, da'awar da al'ummar Bitcoin suke so ya tabbatar bisa sharuddansu wanda ya gagara har yanzu.
Wanda ya kirkiri Bitcoin ya kaura zuwa kauye
A halin da ake ciki, Dailymail UK ta ruwaito cewa Craig Wright ya sayi karamin gida a wani kauye mai ban natsuwa a kasar Burtaniya inda yake da niyyar ci gaba da rayuwarsa duk da cewa dan asalin kasar Australiya ne.
Rahoton ya yi nuni da cewa, sabon karamin gidan da ya gina a 'Beverly Hills' na kauyen Surrey, na da nisa daga birnin da Wright ya taso kuma na da bambanci da inda ya saba a Austaraliya.
'Yan crypto sun tafka mummunar asara yayin da darajar Bitcoin ta dungura kasa
A wani labarin, 'yan crypto sun tafka babban faduwa a ranar Asabar bayan Bitcoin da wasu tsabobin intanet suka rage darajar sama da dala biliyan daya.
Wannan na faruwa ne yayin da 'yan crypto a duniya suka sayar da tsabobin kudaden intanet don daidaituwa da amintattun hannayen jari yayin da bukukuwan Kirsimeti ke gabatowa.
Bitcoin shine mafi daraja a tsabobin kudaden intanet a daraja ta kasuwa, ya fado da 31.6% daga darajar $69,000 mafi girma a shekarar nan a ranar 10 ga Nuwamba.
Asali: Legit.ng