Da dumi-dumi: Kasar Kanada ta sa takunkumi ga 'yan Najeriya saboda bullar Korona

Da dumi-dumi: Kasar Kanada ta sa takunkumi ga 'yan Najeriya saboda bullar Korona

  • Kasar Kanada ta sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ta hamrantawa shiga kasar saboda bullar Korona ta Omicron
  • An samu wasu mutane biyu a Najeriya da suka kamu da sabon nau'in Korona na Omicron a cikin makon nan
  • Akalla kasashe 10 ne kasar Kanada ta sanya a cikin jadawalin haramta shiga akansu, ciki har da Najeriya

Kanada - Kasar Kanada ta sanya dokar hana shigar yan Najeriya kasar a wani yunkuri na dakile yaduwar nau'in cutar Korona na Omicron, Daily Trust ta ruwaito.

Kasar ta Arewacin Amurka da ke samun kwararar bakin haure daga Najeriya ta sanar da hakan ne a safiyar yau Laraba 1 ga watan Disamba.

Ya zuwa yanzu, hukumomin Kanada sun haramtawa kasashe 10 shiga kasarsu saboda bullar sabon nau'in na Korona.

Gwajin Korona
Da dumi-dumi: Kasar Kanada ta sa takunkumi ga 'yan Najeriya saboda bullar Korona | Hoto: NCDC
Asali: Facebook

Kasashen sun hada da Afirka ta Kudu da Namibiya da Lesotho da Botswana da Eswatini da Zimbabwe da Mozambique da Najeriya da Malawi da Masar.

Kara karanta wannan

Korona ta barke a Aso Rock: Garba Shehu, Lai Mohammed, Dogarin Buhari duk sun kamu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ministan Sufuri na Kanada Omar Alghabra, ya ce ‘yan kasashen waje da suka je wadannan kasashe a cikin kwanaki 14 da suka gabata za a hana su shiga kanada na wani dan lokaci.

Ya kara da cewa 'yan kasar Kanada da mazaunan dindindin a kasar wadanda suka kasance a cikin kasashen 10, har ma da wadanda suka yi cikakken rigakafin Korona, dole ne a gwada su kafin su shiga Kanada.

An kuma bayar da rahoton cewa British Columbia ta gano mutum na farko da ya kamu da sabon nau’in Korona, wanda mutumin an ce ya dawo daga Najeriya kwanan nan.

A ranar Larabar nan, Cibiyar Kula da Cututtuka da Yaduwarsu ta Najeriya (NCDC) ta sanar da cewa an gano wasu nau'ikan Korona na Omicron guda biyu a cikin kasar.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana sabon nau'in Korona na Omicron a matsayin "hadari mai girma" a duniya kuma akwai yiwuwar yaduwarsa a duniya.

Kara karanta wannan

Babban Magana: 'Yan Ta'adda Dagar Kasar Waje Na Shirin Kai Hari a Abuja

A halin yanzu ba a san yadda sabon nau'in ke yaduwa ba, yanayin hadarinsa ko yiyuwar jin riga-kafi.

A halin yanzu, nau'in Korona na Omicron ya riga ya fara yaduwa a kasar Netherlands lokacin da Afirka ta Kudu ta sanar da WHO game da hakan a makon da ya gabata, inji rahoton Punch.

NCDC ta tabbatar da bullar nau'in cutar Korona na Omicron a Najeriya

A Najeriya kuwa, Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya, NCDC ta tabbatar da bullar nau'in cutar korona na Omicron da ke firgita kasashen duniya.

Hukumar ta ce an gano mutane biyu da ke dauke da nau'in cutar a halin yanzu. Dr Ifedayo Adetifa, Direkta Janar na hukumar ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannunsa.

NCDC ta ce an gano nau'in cutar biyu ne ta hanyar amfani da fasahar gano tsarin kwayar halita ta 'genomic sequencing'.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sheke mutum 7 a kusa da matsayar sojoji, sun sace wasu a Katsina da Kaduna

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.