An hana yaron Marigayi Muammar Gaddafi neman kujerar Shugaban kasa a zaben Libya
- Hukumar zaben Libya ta haramtawa yaron Marigayi Muammar Gaddafi, Saif al-Islam yin takarar shugaban kasa a babban zaben kasar mai zuwa
- An hana Saif al-Islam da wasu mutane 24 tsayawa takarar shugaban kasar saboda rashin amincewa da takardun takararsu
- Za a dai yi zaben shugaban kasa a kasar a ranar 24 ga watan Nuwamba
Libya - Rahotanni sun kawo cewa hukumar zaben kasar Libya ta fitar da sunan, Saif al-Islam, dan Marigayi Muammar Gaddafi daga cikin masu neman kujerar shugabancin kasar a babban zaben da za a gudanar a ranar 24 ga watan Disamba.
A cewar hukumar, Saif al-Islam na daya daga cikin masu neman takara guda 25 da ta hanawa yin takara saboda rashin amincewa da takardunsu na takara a zaben da za a yi, rahoton Aminiya.
Cikin wadanda suka gabatar da takardun su harda Janar Khalifa Haftar, wanda ya jima yana fafutuka don ganin ya karbe ragamar mulkin kasar, yayin da kotun Amurka ke neman sa ruwa ajallo don fuskantar tuhumar laifuffukan yaki.
Sauran ’yan takarar sun hada da Firaministan rikon kwarya, Abdelhamid Dbeiba da shugaban Majalisar Dokoki da kuma tsohon Ministan Cikin Gida, Fathi Bashagha.
Sashin Hausa na BBC ta rahoto cewa a 2015 wata kotu a tripoli ta yanke wa dan Gaddafi hukuncin daurin kisa sakamakon tarzoman da ya faru a 2011, rikicin da ya hambarar da gwamnatin mahaifinsa.
A wani labari na daban, Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata ya ce dole ne kasashen Afirka ta Yamma da ke fama da rikice-rikice su hada karfi da karfe don ceto yankin daga ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP, PM News ta ruwaito.
Shugaban ya yi magana ne a Fadar Shugaban Kasa dake Abuja, yayin karbar sabon Wakilin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya na Yammacin Afirka da yankin Sahel (UNOWAS), Mista Mahamat Saleh Annadif, dan kasar Chadi.
Buhari ya ce:
“Kai ne makwabcinmu. Kana da kwarewa sosai kan al'amuran da suka shafi yankin Sahel, ka yi shekaru biyar a Mali. Ina fatan za ka sa kasashen su yi aiki tare don tunkarar matsalolin da suka shafe su."
Asali: Legit.ng