Matashi ya samu kyautar N41k yayin da ya mayar da N4m da ya tsinta a lalita a kan hanya

Matashi ya samu kyautar N41k yayin da ya mayar da N4m da ya tsinta a lalita a kan hanya

  • Wani matashi dan shekara 16 ya nuna bajintar da ba kowa ne zai iya ba bayan ya mayar da lalitar da ya tsinta ga mai ita
  • Matashin mai suna Rhami Zeini ya tsinci lalitar wacce ke dauke da dala 10,000 (naira miliyan 4) ne a hanyarsa ta dawowa daga makaranta
  • Zeini wanda aka baiwa dala 100 (N41k) a matsayin tukwici ya bayyana dalilansa na mayar da kudin maimakon boyewa

Wani matashin yaro ya sha yabo da jinjina saboda gaskiya da amana da ya nuna, hakan ya kuma sanya shi kafa tarihi a wani ofishin yan sandan Amurka.

Matashin mai shekaru 16, Rhami Zeini, na a hanyarsa ta komawa gida daga makaranta a Santa Barbara, California lokacin da ya gano wata lalita ajiye a kasa.

Matashi ya samu kyautar N41k yayin da ya mayar da N4m da ya tsinta a lalita a kan hanya
Matashi ya samu kyautar N41k yayin da ya mayar da N4m da ya tsinta a lalita a kan hanya Hoto: Goal Cast
Asali: UGC

A lokacin da Zeini ya bude lalitar, sai ya ga damin kudade na dala 10,000 (naira miliyan 4) a ciki.

Kara karanta wannan

Mai ƙera akwatin gawa ya zama miloniya a dare guda bayan dutse daga sararin samaniya ya faɗo a gidansa

Bai yi wata-wata ba game da matakin da ya kamata ya dauka

A cewar Goal Cast, matashin ya dauki lalitar zuwa ofishin 'yan sanda bayan ya dudduba da kyau ko zai samu wani bayani game da mamallakinta amma bai samu ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da aka tambaye shi kan dalilinsa na dawo da lalitar, Zeini ya fada ma KEYT cewa ya fahimci cewa wannan ne abun da ya kamata yayi.

Zeini ya kara da cewa idan da ace shine a matsayin mai lalitar, ko shakka babu zai so a mayar masa da kudinsa.

“A gare ni, na gano cewa wannan shine abun da ya dace na aikata, idan na dauka sannan na gano mammalakinta, saboda idan nine a matakin sannan abuna ya bata da kudade masu yawa a ciki, na san cewa zan so a dawo mun da shi.”

Kara karanta wannan

Yadda dan Najeriya ya zama sanata a Turai, ya kware a girki, kuma yake so ya gaji Buhari

‘Yan sanda sun yi martani

Jami’an ‘yan sandan sashin Santa Barbara Sheriff sun jinjinawa matashin inda suka bayyana cewa basu taba ganin abu irin haka ba.

Mai lalitar wanda ya batar da ita a gaban wata mota ya baiwa Zeini tukwicin dala 100 (N41k).

Sultan ya yi wa direban da ya mayar da N500,000 da aka manta a kekensa kyautar kudi mai tsoka

A wani labarin kuma, mun kawo a baya cewa Malam Tulu ya tsinci kudi da wasu 'yan kasuwa suka manta a cikin adaidaitarsa har kimanin N500,000.

Sai dai kuma bai yi kasa a gwiwa ba wajen mayarwa da ‘yan kasuwar kudinsu, inda aka yi masa kyautar N5000 a matsayin tukwici.

A yanzu kuma, labari da muke samu daga sashin BBC Pidgin, ya nuna cewa Sultan ya ji dadin wannan gaskiya da Malam Tulu ya nuna inda yayi masa kyautar kudi mai tsoka.

Kara karanta wannan

Ra'ayi: Bidiyon matashin da ya bar sana'a ya koma zaman don kallon jiragen kasa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng