Hauhawar farashin kayan masarufi na iya jefa yan Najeriya milyan 6 cikin talauci a 2021: Bankin duniya

Hauhawar farashin kayan masarufi na iya jefa yan Najeriya milyan 6 cikin talauci a 2021: Bankin duniya

  • Sabbin yan Najeriya milyan shida na gab da fadawa bakin talauci a shekarar nan inji bankin duniya
  • Bankin ya bayyana cewa wannan zai faru ne sakamakon hauhawar farashin kayan masarufi
  • Bincike ya nuna cewa farashin kusan kowani kayan abinci ya tashi yanzu a kasuwa sakamakon wasu dalilai

Amurka - Bankin Duniya ya gargadi gwamnatin Najeriya cewa yan Najeriya milyan shida na iya fadawa cikin bakin talauci sakamakon hauhawar farashin kayan abinci.

Bankin wanda ke zamansa a Amurka ya shawarci gwamnatin Najeriya ta dau matakin gaggawa.

A watan Yuni, bankin yace a 2020, akalla yan Najeriya milyan 7 suka fada cikin talauci sakamakon hauhawar farashin abinci kadai.

Bankin ya yi amfani da binciken National Longitudinal Phone Survey (NLPS) wajen ganin illar cutar COVID-19 kan rayukan mutane da jin dadin iyalai, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Muna ciyar da dalibai milyan 9 kulli yaumin a Najeriya, Minista Sadiya Farouq

Binciken NLPS wani hadin kai ne dake gudana tsakanin hukumar lissafin Najeriya NBS da na bankin duniya.

Hauhawar farashin kayan masarufi na iya jefa yan Najeriya milyan 6 cikin talauci a 2021: Bankin duniya
Hauhawar farashin kayan masarufi na iya jefa yan Najeriya milyan 6 cikin talauci a 2021: Bankin duniya

A cewar rahoton bankin:

"Hauhawar farashin kayan masarufi tsakanin Yunin 2020 da Yunin 2021 na iya jefa wasu sabbin mutum milyan shida cikin talauci, musamman wadanda ke birane."
"Wannan bincike ya nuna cewa masu fama da bakin talauci a Najeriya ya kari daga 40.1% zuwa 42.8% sakamakon hauhawar farashin abinci tsakanin Yunin 2020 da Yunin 2021."
Hakan na nufin cewa karin yan Najeriya milyan 5.6 zasu sake dilmiya cikin talauci. Yanzu talauci na kan zama ruwan dare a Najeriya."

Rashin tsaro, ambaliya da dalilai 4 da suka jawo tsada da hauhawan farashin abinci

Abubakar Sani Abdullahi ya yi rubutu na musamman, inda ya yi bayani a game da abubuwan da suka haddasa tashin kayan abinci a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda iyayen matashi suka nuna farin ciki mara misali yayin da ya duba sakamakon jarrabawar zama lauya

Abubakar Sani Abdullahi malami ne a sashen kula da noma da tattalin arzikin kasa a cibiyar binciken harkokin noma ta Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

Legit.ng Hausa ta kawo wannan rubutu da masanin tattalin harkar noma ya yi a shafinsa

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng